Wahalar mulkin APC 2023 yan Nijeriya zasuyi hukunci tsakanin PDP da APC

Wahalar da APC taba yan Nijeriya 2023 yan Nijeriya zasuyi hukunci tsakanin PDP da APC
Inji Labaran Maku
Daga Zubairu Lawal
Jagorar yakin niman zaben Dan Takarar Shugabancin Nijeriya Alhaji Atiku Abubakar da Dan Takarar Gwamnan jihar Nasarawa Hon. Devid Emmanuel Ombugadu na inuwar Jam’iyyar PDP Hon.Labaran Maku ya bayyana haka a taron manema Labarai a karamar Hukumar Karu. A lokacin kaddamar da yakin niman zaben Jam’iyyar PDP a fadin jihar wanda zai fara ranar Littinin a garin Toto.
Labaran Maku yace; Jam’iyyar APC dake mulkin jihar Nasarawa tana hanyar hada shekara 12 sannan Jam’iyyar APC a Nijeriya suna hanyar hada shekara 8 amma gabaki dayansu babu abinda suka tsinanawa al’umman a kasan.
Hon. Maku yayi kira ga al’umman Nijeriya dasu fito kwai da kwarkwata su zabe Alhaji Atiku Abubakar domin shine zai fitar da al’umma daga kangin da ake ciki.
Hon. Maku yace; yanzu al’umman jihar Nasarawa sun dandana kudansu a mulkin APC, basu fatan su sake zabenta.
Ya kuma kalubalanci Jam’iyyar APC da cin hanci da rashawa babu abinda suka kawo na cigaba a tarayyar Nijeriya.
Yace; kamar yadda Alhaji Atiku Abubakar zai kawo cigaba mai amfani a Nijeriya hakama Hon.Devid Emmanuel Ombugadu zai kawo cigaba mai yawa da zai amfani jama’an jihar Nasarawa.
Labaran Maku yace; bazaiyi karyaba kowa yasan an samu chanji na wahala a mulkin APC a Nijeriya.
Saboda a shekarar 2015 kowa yasan farashin man petur yana N87 amma yanzu N250. Hakama a 2015 Buhun shinkafa yana N8000, amma yanzu N42000, sannan Dalar Amurka a 2015 tana N150, amma yanzu 750.
Yan Nijeriya su zasuyiwa kansu hukunci  a zaben 2023 tsakanin PDP da APC.
Shima a nasa jawabin Shugaban Jam’iyyar PDP ta jihar Nasarawa Hon. Francis Orugu, yayi kira ga Jam’iyyar APC dasu fara tattara kayansu daga jihar Nasarawa domin lokaci yayi da PDP zai karbi mulkin jihar ta kawo gyara.
Dan Takarar Gwamnan jihar Nasarawa na Jam’iyyar PDP Ho. Devid Emmanuel Ombugadu. Ya jaddada kuddurinsa na kawo cigaba ga al’umman jihar Nasarawa.
Yace; ahirin bunkasa harkan noma da tattalin arziki da Samar da ayyukanyi ga matasa, da bunkasa harkan ilumi shine kuddurinsa.
Ombugadu yace; kuddunirsa dayace; amma tana tattar da abubuwa dabam dabam masu amfani. Idan har jama’a suka zabe shi ya zama Gwamnan jihar zai bunkasa ayyukan da kowa ya shigo jihar Nasarawa zai tabbatar da ta amsa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *