Gwamna Abdullahi Sule ya yabawa Rundunar NAYES kan kama mace da Bindiga AK47
Daga Zubairu Lawal
Gwamnan Jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule yace; Rundunar tsaro ta fari kaya da Gwamnatin Jihar Nasarawa ta samar daga matasan jihar suna taka muhammiyar rawa.
Yace; Rundunar ta NAYES Wanda suke karkashin kulawan Gwamnatin Jihar suna taimakawa jami’an tsaro kamar Yan Sanda da NSCDC da sauransu.
Da yake jawabi wajen bikin yaye Rundunar Matasa sabobin dauka kimanin 250, Gwamna Abdullahi Sule Wanda ya samu wakilcin Sakataren Gwamnatin Jihar Alhaji Aliyu Ubandoma.
Yace; tunda farko Gwamnati ta kirkire wannan Rundunarce domin taimakawa Jami’an tsaro. Kuma suna aiki kafada da kafada.
Akwai Bangaren kula da tsaro da masu kula da zurga zurgan ababen hawa a jihar, da Kuma masu kula da gandun daji.
Yace; da gudumawar NAYES cikin zaman lafiya da ake samu a jihar Nasarawa.
Shima a nasa jawabin Shugaban Rundunar NAYES ta jihar Nasarawa Alhaji Abdullahi Labaran Maina.
Yace; yana godiya ga Allah da ya sanya ake samun yabo na musamman daga Gwamnatin jihar kan wannan Rundunar ta NAYES.
Yace; Rundunar NAYES tana gudanar da ayyukan ta da hadin giwan Rundunar yan Sanda da sauransu.
Yace; duk lokacin da suka kama masu laifi suna mikasune ga Rundunar yan Sanda ko NSCDC, domin garzayawa dasu Kotu.
Yace; Rundunar NAYES tana da mutani kimanin 4500 a fadin jihar. Kuma ana biyansu N10,000 duk wata.
A lokacin da aka kirkire Hukumar yan Sandan farin kaya ta jihar, Gwamna Abdullahi Sule ya bukaci mubada yara 250 cikin Rundunar NAYES.
Shi ya sanya a yanzu muka tantance wasu mutani 250 muka maye gurbinsu.
Abdullahi Labaran Maina ya bayyana irin nasarorin da Suke samu. Yace ; a kwanaki Rundunar ta kama wata mata a Wamba dauke da Bindiga kirar AK47 da albarusai 200 a Rugar fulani kuma daga jihar Zamfara take. Kuma sun mikata ga hukumar DSS.
Haka zalika sun kama wani mutum da ya sato mota daga jihar Ondo a nan garin Lafia.
Sannan suna kama wani mutum a garin Nasarawa da Bindiga kirar AK47 da Albarushi . a Doma suna kama yaran Fulani 4 da Bindiga kirar gargajiya, duk sun mikasu ga yan Sanda.
Labaran maina yace; suna aiki kafada da kafada da duk Jami’an tsaro dake jihar kuma suna girmama juna.