Shekara 16 yan adawa sukeyi mulki basu tsinana komai ba a Nasarawa – Gwamna Abdullahi Sule
Daga Zubairu Lawal
Masu adawa da ke cewa bamuyi aikin komai ba. Suyi tunani Shekara 16 suna rike da mukaman Gwamnati amma basu iya tsinana komai a laukansu ba.
Zuwanmu Gwamnati mukayi tituna har kofan gidansu.
Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana cewa Insha Allah zasu dawo mulki a jihar Nasarawa 2023.
Gwamna ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da gangamin yakin niman zabe a garin Keffi.
Gwamna yace wannan filin da muke taro a cikinsa, yana hade da filin da a baya ake gudanar da harkokin kasuwanci da sauransu.
Zuwanmu muka gina kasuwa ta zamani muka gina filin taro muka samar da mizishal mai girman gaske.
Kasuwannan da muke ginawa irin wannan akwai a garin Akwanga Nasarawan Eggon da sauransu.
Yanzu haka muna da kamfanin da za arika samar da shuga da zai dauki ma’aikata Sama da 30,000.
Jihar Nasarawa jiharce da mukeda albarkatun kasa, da tarin arziki da Allah ya bamu.
Cikin ayyukan da muka gabatar akwai hanyoyin Sisin baki da sauransu. Ga tagwayen titin da mukeyi zuwa gaba da gidan Gwamnati Lafia.
Masu cewa bamuyi komaiba. Shekara 16 sukayi basuyi komai ba. Ko rijiyar Burtsatse basu samar a yankunansu ba.
Gwamnan ya mikawa yan takara uku tuta. Dan majalisan wakilai na tarayya da yan majalisan Dokokin jihar guda biyu.
Akwai maganar Matawalle da Shehu Tukur a Kotu. Saboda haka bazamu baiwa kowa tuta ba.