*Allah ya sani yan Nijeriya sun gaji da mulkin APC Inji Shugaban PDP Nasarawa*
Daga Zubairu Lawal
Allah ya sani al’umman Nijeriya sun gaji da mulkin APC. Yanzu kowa baya bukatan APC jama’an jihar Nasarawa basu son APC. Allah ma baya son APC.
Saboda jam’iyyar APC sun jefa al’umman Nijeriya cikin mawuyacn wahala da yunwa da talauci.
Yunwa na kashe musulmai yana kashe kirista. Babu Wanda wahalar APC ta bari a tarayyar Nijeriya, maza da mata manya da yara suna jinjiki.
Ya zama darashi ga al’umman Nijeriya su daina maganar bambamcin addini ko kabilanci wajen zabe.
Shima a nasa jawabin Hon. Labaran Maku yayi kira ga al’umman jihar Nasarawa dasu giji kariya da yaudara irin na APC.
Hon. Maku yace tunda APC suka hau mulki babu abinda suka kawo Nijeriya sai koma baya. A jihar Nasarawa babu aikin kirki.da APC sukayi.
Duk wasu ayyukan cigaba a jihar Nasarawa PDP sukayi. Gina Sakatariyyar Gwamnatin tarayya da Kwalajin kimiyya da fasaha da Asibitin Gwamnatin tarayya da Jami’ar Jihar Nasarawa da Jami’ar Gwamnatin tarayya da hanyoyin Doma zuwa Lafia zuwa Awe da Babban Bankin Nijeriya duk Gwamnatin PDP ne sukayi.
Babu aiki kwara daya daga Gwamnatin tarayya da APC tayi.
Yace Jam’iyyar APC ta jefa al’umman Nijeriya cikin fitintunu matsala tsakanin manuma da makiyaya. Babu zaman lafiya.
Hon. Labaran Maku yace; Canji ya zama dole a jihar Nasarawa, saboda kowa yaga taron Atiku Abubakar a Nasarawa, yasan jihar Nasarawa ta PDP ce.
Yanzu Jam’iyyar APGA da PDP sun hada kai a Nasarawa domin kawo sauyi mai amfani da gina jihar Nasarawa.