Zamu inganta harkan ilumi a Nijeriya – kwankwaso
inji Kwankwaso.
Daga Zubairu Lawal
Dan takarar Shugaban kasa a Jam’iyyar NNPP Injiniya Rabi Musa Kwankwaso yace; idan al’umman Nijeriya suka zabeshi ya zama Shugaban kasa zai bada mahimmanci a bangaren Ilumi.
Kwankwaso yace; duk dan talaka da dan mai kudi zasuje makarantan Gwmnati kyauta.
Yace; zasu bada ilumi kyauta, kuma babu batun biyan kudin jarabawar WAEC da NECO da JAMB. Ya kara da cewa duk dalibin da ya rubuta jarabawar JAMB idan bai samu gulbin shiga Jami’a a wannan shekarar ba, JAMB ba zata lalaceba sai ta kai tsawon shekara hudu.
Kwankwaso yace zasu baiwa matasa miliyoyin nairori maza da mata domin bunkasa Harlan kasuwanci.
Kwankwaso ya bayyana hakane a wajen yakin niman zaben Dan takarar Gwamnan jihar Nasarawa a karkashin jam’iyyar NNPP Hon. Abdullahi Yakubu mai Doya a garin Keffi.
Kwankwaso yace; Jam’iyyar NNPP ta shirya tsarin taimakawa al’umman Nijeriya saboda suna cikin mawuyacin hali.
Shima a nasa jawabin Dan takarar Gwamnan jihar Nasarawa karkashin jam’iyyar NNPP Hon Abdullahi Yakubu mai Doya yace; babban kuddurinsa idan ya zama Gwamnan jihar Nasarawa zai tabbatar da zaman lafiya.
Kuma zai samar da bangaren da zai warema Fulani suma suyi kiwo saboda a samu wadacecen nama da madarar shanu da al’umman jihar zasu amfana.
Hon. Abdullahi Yakubu mai Doya yace; cikin shirye-shiryen shi akwai bunkasa harkan ilumi na kimiyya da fasaha ga matasan jihar Nasarawa.
Hon. Abdullahi Yakubu mai Doya yayi kira ga al’umman jihar Nasarawa dasu fito ranar zabe su zabe jam’iyyar NNPP.