Magaji ya kalubalanci masu kira da a sauki Shugaban APC na kasa.
Daga Zubairu M Lawal Lafia
Jigo a siyasan Jihar Nasarawa tsohon Dan takarar kurar Sanata a Jam’iyyar APC a mazaver Nasarawa ta yamma Hon. Barista Labaran Shu’aibu Magaji Matawallen Toto. Ya kalubalanci masu kokarin kira ga Shugaban Jam’iyyar APC ta kasa Sanata Abdullahi Adamu cewa ya sauka daga mukaminsa.
Hon. Labaran Magaji yace; masu wannan maganar suyi tunani bai kamata ace wanan maganar na fita daga bakin ya’yan Jam’iyyar APC ba.
Ya yi kira ga masu fada aji na Jam’iyyar APC dasu kwabi masu furta wannan kalamai na cewa Shugaban Jam’iyyar ya sauka.
Yace:rawar da Shugaban Jam’iyyar APC Sanata Abdullahi Adamu ya taka wajen hada kan Jam’iyyar APC da dukkan mambobinta har ta samu nasara ,zaven Shugaban qasa da samun kuneru masu yawa a Majalisan Dattijai da wakilai. Abin a yana masa ne.
Hon. Magaji ya bukaci uwar Jam’iyyar APC ta kasa data kyale Sanata Abdullahi Adamu ya cigaba da jagorancin Jam’iyyar zuwa shekarar 2027.
Haka zalika ya bayyana cigaban da Jam’iyyar APC zata samu a zaven Gwamnonin da za a yi ranar 18 ga wata.
Magaji ya bayyana hakane lokacin da yake zantawa da tsofin kansilolin Jihar Nasarawa dan gane da zaven Gwamna Abdullahi Sule a garin keffi.
Ya kuma yi kira ga al’umman jihar Nasarawa da su baiwa Gwamnan goyon baya saboda cigaban ayyukan alheri.