KURI’UN BOGE Shugaban Karamar Hukumar ya shiga Hannu a Jihar Nasarawa
Daga Zubairu Lawal
Hukumar Tsaro ta farin kaya DSS ta kama Shugaban Karamar Hukumar OBI dake Jihar Nasarawa Hon. Joshua Zheyekpuwudu da tarin takadun zabe na Boge Wanda an dangawa shi.
Lamarin ya farune a yau Asabar 18/3/2023 a zaben Gwamnoni da yan Majalisun dokoki da yake gudana.
Jami’an tsaron sun kama Shugaban Karamar Hukumar ne a Unguwar Tudun Kwauri dake Lafia a kan hanyarsa ta zuwa inda zashi.
A halin yanzu dai Shugaban Karamar Hukumar Hon.Zheyekpuwudu yana hannu jami’an tsaro. Sai dai a Jihar Nasarawa ana gudanar da zabe lami lafiaya.