Majalisar Dinki Duniya ta yabawa yan Nijerya kan yadda suka gudanar da zabe lafiya

Majalisar Dinki Duniya ta yabawa yan Nijerya kan yadda suka gudanar da zabe lafiya
Daga Zubairu Lawal
Majalisan Dinkin Duniya ta yaba da rawar ganin da al’umman Nijeriya suka taka na gudanar da zaben 2023 lami lafiya.
Da yake jawabi Manzo na musamman da ya wakilci Babban Sakatare Janar na Majalisan Dinkin Duniya wajen sulhunta yan takarar Shugabancin Nijeriya mutum 18 a zaman da ya gudana a garin Abuja ranar 23/2/2023.
Mr Giovanie Bihar wada shike gudanar da manyan ayukan Majalisan Dinkin Duniya a nahiyar Afirka ta yamma. Yace; duk yan takarar sun amince da yadda da nasara ko akasin haka matukar aka gudanar da sahihin zabe.
Kuma sun yarda da cewa zasu gargadi magoya bayansu da gujewa kawo rikici da zai janyo asarar rayuka a kasa.
Mr.  Giovanie Bihar yace; cikin ikon Allah an gudanar da zabe ba tare da samun hatsaniya ko tashin hankali ba, duk da cewa sauran yan takarar sun koka kan yadda zaben ya gudana.
Yace: al’umman Nijeriya sun nuna wayewa da sanin ya kamata. Yace: sun gudanar da zaben da babu asarar rayuwa da dukiyoyi Wanda hakan yayiwa Duniya dadi.
Yace: kwamitin kula da zaman lafiya   National Peace
Committee (NPC).  tayi alfahara da wannan zaben yadda akayi lafiya aka gama lafiya.
Yace; zabubukar da suka gudana na 2023 a Nijeriya kama daga matsayin Shugaban kasa da yan Majalisan Dattawa da na Majalisan Wakilai da Gwamna da Majalisan Dokoki na jihohi duk ya bada ma’anna yadda aka gudanar lafiya.
Mr.Giovanie Biha yace; a matsayin masu sanya ido akan zaben sun jinjinawa hukumar zaben Nijeriya karkashin jagorancin Farfesa Mahammu Yakubu da tawagarsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *