Dole sai mun kula da al’umman dake rayuwa cikin kunci a Arewa maso gabas – Inji Mr.Matthias Schmale

Dole sai mun kula da al’umman dake rayuwa cikin kunci a Arewa maso gabas – Inji Mr.Matthias Schmale
Daga Zubairu Lawal
 
Babban abinda yake cimana turo a kwarya shine irin matsalolin rashin kulawa da bada mahimmanci ga rayuwar al’umman dake rayuwa cikin kunci a sansanonin gudun hijira dake yankin Arewa maso gabashin Nijeriya.
 
Mr.Matthias Schmale shine Babban kodineton kula da halin da marasa galihu ke ciki a ofishin Majalisan Dinkin Duniya.
 
Yace; al’umman yaken Arewa maso gabas dake arewacin Nijeriya ke ciki dole mu mai da kulawanmu garesu.
Yace; Majalisan Dinkin Duniya zata farfado da asusun neman taimako na musamman da zai kai dalar Amurka 1.3 biliyon domin ceto rayuwar moliyoyin mutani dake rayuwa a sansanonin gudun hijira a yankin.
Yace: a cikin shekaru 13 yanzu haka akwai kimanin mutanin da yawansu yakai miliyon 5.5 da suke gudanar da rayuwa cikin kunci sakamakon hare haren ta’addanci da mayakan Boko Haram da sauransu suka jefa mutanin yan kin.
Yace: cikin kashi tamanin na al’umman kauyakun Adamawa da Borno da Yobe suna rayuwanne a sansanonin yan gudun hijira. Rayuwa na kunci.
Sannan duban dubatan mutanin Bama dake jihar Borno tuni suka ketara zauwa makwafta.
Yace; akwai kananan yara da suka haura
300.000 dake zama babu zuwa neman ilumi. Suna gudanar da rayuwarsu ne a sansanonin gudun hijira a Maiduguri.
Sanan da damansu kauyukansu ya zama kufayi sakamakon hare haren Bama bamai na yan Ta’adda. Yanzu ko zasu koma basu da matsugunai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *