Ranar Alhamis Mai Zuwa INEC Za Ta Bayyana Sakamakon Zaben Jihar Adamawa

Ranar Alhamis Mai Zuwa INEC Za Ta Bayyana Sakamakon Zaben Jihar Adamawa

A ranar Alhamis ne hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC za ta bayyana sakamakon zaben gwamnan jihar Adamawa mai cike da cece-kuce da ban mamaki, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) za ta yi zama a tsakanin ranakun Talata da Laraba akan lamarin, kamar yadda kwamishinan labarai na kasa kuma shugaban kwamitin wayar da kan masu kada kuri’a, Dakta Festus Okoye, ya bayyana.
A ranar Litinin din da ta gabata ne hukumar ta dakatar da kwamishinan zabe na jihar Adamawa, REC, Mista Hudu Yunusa-Ari saboda kwace ikon babban jami’in zaben kan shirme da rikicin da ya hada na sanar da sakamakon zaben jihar ba tare da an kammala tattara sakamakon zabe ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *