Gwamna Abdullahi Sule yayi kira ga Musulmai suyi amfani da darusan Ramadan
Daga Zubairu Lawal
Gwamnan Jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule yayi kira ga Musulmai musamman na Jihar Nasarawa da Kasa baki daya da suyi amfani da abubuwa da suka koyo daga watan Ramadan.
Gwamnan yace; Musulmai sun gudanar da Azumi 29 cikin watan inda suka rikayin ibadu badare ba rana.
Wannan Babban watane da yake cike da darusa masu mahimmanci.
Yace; ya kamata abubwan da aka gudanar a watan Ramadan a cigaba da gudanar dashi masamman adu’o’in zaman lafiya da yawaitan arziki.
A cigaba da kyautatawa juna yadda akeyi a cikin watan Ramadan.
Saboda a watan Ramadan mai azumi baya fatan ya cutar da kowa yana bukatar ya kyautatama Wanda ba Musulmai ba.
Gwamnan Sule; yayi kira ga al’umman Jihar Nasarawa dasu rugumi akedar zaman lafiya saboda zaman lafiya shina cigaban kowata kasa da al’umman cikinta.
Yace: a koda yaushe yana duba yadda kasar Labano ta kasance lokacin da ta fada rikicin addanin. Yace; anyi asarar rayuka Mara adadi, an lalata komai na cigaba da more rayuwa.
Gwamnan ya tabbatar da Samar da cigaban Jihar Nasarawa da al’umman cikinta.