Marie Josiane kenan “Yar Kasar Rwanda da ta auri tagwaye kamar ni……………
Dama dai ance tagwayen sun dade suna komi tare saboda tsanani shakuwar su, har kuma suka yi dacen auren mace daya
Marie tace ta fara sanin Usainin cikinsu ne har sun fara tsananin abota sun ma yi shawarar aure, kwatsam wata rana tazo wajensa kaman yanda ta saba ta wuce straight ta sumbaceshi sai daga baya ta gano ashe dan’uwan saurayinta ne, kuma bata taba sanin su biyu bane
Daga wannan sumbata shi kuma gogan naka shima ya kamu da sonta, karshe dai suka zauna meeting su ukun suka yanke shawarar kulla auren ta su dukan
“Yau kusan Shekaru biyu kenan da wannan yarjejeniya ina zaune da su a matsayin mazajena na aure kuma ko kadan ba a taba samun sabani ba tsakanin mu, muna zaune lami lafiya da juna” in ji Amarya Marie
Maganar da akeyi ma yanzu haka ciki gareta kuma suna cikin murna za a haifo masu da me uba biyu uwa daya .