Arteta ya nemi yafiyar magoya baya kan shan kayen Arsenal a hannun Brighton

Arteta ya nemi yafiyar magoya baya kan shan kayen Arsenal a hannun Brighton

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Mikel Arteta ya nemi afuwar magoya baya dangane da bugun da kungiyar ta sha har gida a hannun Brighton da kwallaye 3 da nema, rashin nasarar da ke sallama tseren da kungiyar ke yi a kokarin lashe kofin Firimiya tsakaninta da Manchester City.Gunners dai ta shafe tsawon lokaci ta na jagorancin teburin gasar ta Firimiya, a kokarin kawo karshen dakon shekaru 19 da ta yi a baya don kai kofin gida, to sai dai a watannin baya-bayan nan ta gamu da gagarumin matsin lamba daga City wadda ta lashe kofunan har sau 11.

Wasanni 2 cikin 7 da Arsenal ta doka a baya-bayan nan kadai ta iya nasara, Wanda ken una yiwuwar bankwananta da kofin na Firimiya dai dai lokacin da ake da tazarar maki 4 tsakaninta da City, kuma tawagar ta Guardiola ke da wasa guda a hannu.

A jawabinsa gaban manema labarai Arteta ya ce salon wasan da Arsenal ta yi a zagaye na biyu na haduwar ta jiya sam ba abin karba ba ne.

A cewarsa a lissafe, iya lashe kofin na Firimiya ga Arsenal har yanzu abu ne mai yiwuwa amma a yanzu abin da ya fi muhimmanci garesu shi ne samar da gyara ga kura-kuren da suka yi a jiya.

Idan har Arsenal ta gaza nasara a haduwarta da Nottingham Forest a lahadi mai zuwa, kuma City ta yi nasara kan Chelsea a ranar 21 ga watan nan, kai tsaye tawagar ta Pep Guardiola ta lashe kofin karo na 5 cikin shekaru 6.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *