Gwamnatin Nasarawa zata kirkiro yan kwallon kafan U-13 na musamman a jihar- Gwamna Sule

  1. Gwamnatin Nasarawa zata kirkiro yan kwallon kafan U-13 na musamman a jihar.  – Gwamna Sule
    Daga Zubairu Lawal
    Gwamnan jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule ya sha alwashen cewa Gwamnatinsa zata kirkire kungiyar yan kwallon kafa na yan qasa da shekaru 13 ( U-13) da zasu zamanto na musamman da  zasu rika wakiltar jihar a gasar wasan kwallon kafa a kasa.
    Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana hakane a wajen kammala gasar kwallon kafa na yan qasa da shekaru 13 wanda gidauniyar Sakataren Jam’iyyar APC Alhaji Aliyu Bello ta shirya.
    Da yake magana a madadin Gwmnan jihar Nasarawa Mataimakin Gwamna Dakta. Emmanuel Agwadu Akabe.
    Yace; yadda wannan gasar ta kayatar da Gwamnatin jihar da al’umman jihar, yaga yadda ko ina ake annasuwa. Ya karawa Gwamnatin kwarin giwar samanar da kungiyar kananan yan kwallon kafa masu tasowa a jihar.
    Dakta. Akabe. Yace; Gwamnati zata zakulo kwararu biyar biyar a kowata karamar hukuma cikin kananan hukumomi 13 a fadin jihar.
    Zata Samar da kungiyar yan kwallon kafa da za ayi alfahari dasu nan gaba ba a jihar ba harma da kasa baki daya.
    Gwamnatin jihar Nasarawa ta yabawa Gidauniyar Alhaji Aliyu Bello saboda yadda take kulawa da rayuwar matasa da yara kanana a fannin ilumi da harkokin more rayuwa.
    Shima a nasa jawabin Shugaban gidauniyar kuma Sakataren Jam’iyyar APC reshen jihar Nasarawa. Alhaji Aliyu Bello yace; an shirya wannan gasar ne. Domin nishadantarwa ga Dalubai yan Piramare dake fadin jihar Nasarawa.
    Wannan gasar kwallon kafa zai kara basu sha’ awar  zuwa makaranta. Kuma zasu kulla zumunta na abokantaka tsakaninsu. “Yaro zaiyi alfahari da yazo kuma ya buga U-13 na Jihar”.
    Kananan hukumomi 13 suka samu fafatawa a gasar. An buga wasan niman rukune na daya zuwa na uku a rana daya ranar yara na duniya 27-5-2023 a filin wasa na Jami’ar Gwamnatin Tarayya dake garin Lafia.
    Kungiyar kwallon kafa ta Lafia sukazo mataki na uku bayan sun doke Keffi da ci daya.
    Kungiyar Kokona sun zo na biyu bayan da sukasha kashi da ci daya mai ban haushi a hannun Kungiyar Wamba.
    Mataimakin Gwamna Dakta Emmanuel Akabe da Tsohon Gwamnan jihar Nasarawa Sanata Umar Tanko Al-makura da Sakataren Gwamnatin jihar Nasarawa Barrister Aliyu Uban Doma da Sabon Sanata Alhaji Aliyu Ahmad Wadada ne suka mika kyaututuka ga kungiyoyin da sukayi nasara.
    1. Kungiyar kwallon kafa ta Wamba ta samu Babban kofi da N200,000
    2. Kungiyar kwallon kafa ta Kokona ta samu Karamin kofi da N150,000
    3. Kungiyar kwallon kafa ta Lafia ta samu karamin kofi da N100.000
    Wasan na karshe ya tara manyan yan siyasan jihar da masu fada aji a fadin jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *