Raddi ga Hafsoshin tsarom kaaa- Marasa gaskiya ke ihun a cire Nuhu Ribadu daga matsayin NSA na Tinubu

Yadda Manyan Hafsoshin Sojin Najeriya suka matsawa Tinubu lamba kan ya sauke Nuhu Ribadu a matsayin mai ba shi shawara kan harkokin tsaro, suna mai cewar ba za su yi aiki da karamin su ba

Tinubu ya nada Nuhu Ribadu tsohon shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC a matsayin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, amma saboda matsin lamba daga wasu manyan hafsoshin soji Hakan yaci tura, a yanzu Yana ma tsayin mai bada shawara akan harkokin tsaro (SA), SaharaReporters ta samu labarin.

Majiyoyi sun shaida wa SaharaReporters a ranar Alhamis cewa manyan hafsoshin soji sun shaida wa Shugaba Tinubu a fili cewa ba za su iya yin aiki da “karaminsu” a matsayin NSA ba, don haka suka yi fatali da ra’ayin nada shi.

Manjo-Janar Babagana Monguno (ritaya) a halin yanzu shi ne NSA na Najeriya, ya gaji Kanar Sambo Dasuki (mai ritaya) – lamarin da ke nuna yadda manyan hafsoshin soji da suka yi ritaya suka mamaye ofishin.

“An riga an zabi Ribadu a matsayin NSA, amma jami’an soji masu karfi sun ce ba za su iya aiki da karaminsu ba, kuma duk wanda ba tsohon Janar na soja ba, ba za a yarda da shi ba a wurin sojoji,” wata majiya daga fadar shugaban kasa ta bayyana wa SaharaReporters. .

Ribadu, mai shekaru 62, ya fito ne daga Yola, jihar Adamawa. Shi ne shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasar, EFCC, kuma kwamishinan ‘yan sanda ne mai ritaya.

Ya kasance shugaban kwamitin tattara kudaden shigar man fetur.

Rahoton SR

#DailyTrueHausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *