Gwamman Zamfara Ya Karrram Hajiyar Da Ta Tsinci Dala 80,000 A Saudiya Ta maida Wa Maishi
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, A yau Alhamis, ya karrama Hajiyar da ta mayar da kudin da ta tsinta dala 80,000 a aikin Hajjin da ya gabata a kasar Saudiyya.
Mahajjatiyar, Hajiya Aishatu ‘yan Guru Nahuce daga karamar hukumar Bungudu ta samu dala 80,000 wanda yayi daidai da kudin Nigeriya (N64,240,000) sannan ta mika ta ga jami’in hukumar jin dadin alhazai ta Zamfara domin maida wa mai shi.
Mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris, ne ya bayyyana haka a takardar da ya sanya mahannu ga manema labarai yau a Gusau.
Acewar sa,Gwamnan ya kuma bayyana matukar farin cikin sa da gwamnatin jihar ta nuna akan kyakyawan halin Hajiya Aisha da ta maida kudin.
“Dukkan al’ummar jihar Zamfara suna alfahari da farin ciki kan abin da Hajiya A’ishatu ta yi a Saudiyya,ta karawa Jihar mu da Kasa baki daya kima da daraja a Idan duniya.
“Mun ga kyakyawan misali karara na gaskiya da ya kamata a yi koyi da Hajiya A’isha, dan ba kowa ne zai iya samun irin wadannan makudan kudade a wurin da ba kowa, ya mayar da su.
“Dan haka gwamnatin jihar Zamfara za ta yi iyaka kokarinta don taimakawa iyalan Hajiya Aisha.
“Shugaba Bola Ahmed Tinubu kuma zai karrama Hajiya A’isha bisa wannan aiki na gaskiya.”
Tun da farko, Sarkin Bungudu, Alhaji Hassan Attahiru yayin gabatar da Hajiya A’isha, ya jaddada cewa, matakin da ta dauka ya kara kara mutunta al’ummar Zamfara baki daya.
Hajiya Aisha ta bayyana godiyar ta akan karamci da akai mata tunda Kasar Saudiya da yau anan Gusau.