Masu aikata lefi zasu yabawa aya zaki a jihar Nasarawa
Inji Kwamishinan Shari’a
Daga Zubairu Lawal
Hon. Barrister Labaran Shuaibu Magaji (Matawallen Toto) Kwamishinan Shari’a ya bayyana hakane a lokacin da ya kai ziyara ga Alkaline – Alkalai na jihar Nasarawa Justice Aisha Bashir Aliyu.
Kwamishinan yace; makasudin ziyarar da tawagar Ma’aikatan Shari’a ta jihar ta kawo zuwa Ofishin Alkalin Alkalai na jihar,
sun zo ne domin hadin giwa wajen magance duk wani matsalolin Shari’a a fadin jihar Nasarawa.
Barrister Magaji yace; Gwamna Abdullahi Sule mutumne mai mutumta dokoki na Shari’a. kuma yana fifita al’umman jihar Nasarawa da kare martabarsu.
Saboda haka babu yadda za a kyele masu aikata meyagun lefuka suna takurama al’umma a cikin jihar.
Kwamishinan yace; duk Wanda aka kamashi da aikata lefi zai yabawa aya zaki Gwamnati bazata kyele shi ba kowaye.
Kwamishinan yace; Ma’aikatan Shari’a ta shirya fuskantar kalubalantar duk Wanda yake kawo barazana ga zaman lafiyan jihar Nasarawa.
Kwamishinan yayi kira ga al’umman jihar Nasarawa dasu baiwa Gwamnati da Ma’aikatan Shari’a hadin kai wajen hukunta duk wani mai lefi.
Itama a nata jawabin Babban Alkalin Alkalai na jihar Nasarawa Justice Aisha Bashir Aliyu tace; babu shakka hukunci na Shari’a zai taimaka wajen magance aikata miyagun lefuka a kasan nan.
Tace; wannan tsarin zai baiwa duk wani mazaunin jihar Nasarawa damar nimawa kansa yanci a bangaren Shari’a.
Tace; mutani zasu fahici kusanci da San in yanci idan har Shari’a zata kwatawa mutum hakinsa.
Mai Shari’ar ta yaba da wannan ziyarar ta kuma baiwa Ma’aikatan Shari’ar shawarwari ta yadda zai kawo cigaba ga Gwamnatin jihar da al’umman jihar baki daya.
Ta kuma bada shawarwarin hanyoyin sulhunta jama’a koda tsakaninsu da Gwamnati ne, domin tabbatar da zaman lafiya da fahintar juna.