Rundunar yan Bangar Fulani sunyi nasara kwato Wanda akayi Garkuwa da shi a Nasarawa
Daga Zubairu Lawal Lafia
Kungiyar ƴan Banga ta Makiyaya (NOMAD VIGINALTE NIGERIA) ta yi nasarar kuɓutar da wani mai suna Bashir Muhammad kwanaki kaɗan da kaddamar da kungiyar a jihar Nasarawa
Kwamandan Kungiyar na jihar Nasarawa Alhaji Akajo A. Gyara ne ya jagoranci kuɓutar da Bashir daga hannun masu garkuwa da mutane bayan sunyi garkuwa da shi ranar Asabar a yankin Gitata dake karamar hukumar Karu jihar Nasarawa.
Idan za a iya tunawa dai ranar Laraba 17 ga watan Janairu 2024 shugaban kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore na kasa Bello Abdullahi Bodejo ya jagoranci kaddamar da mutum 1,144 karon farko na kungiyar a garin Lafia.