Rundunar Sojan saman Nijariya ta jajantawa Gwamnatin Nasarawa bisa kisan mutani 37 da sojan sukayi kan kuskure

Rundunar Sojan saman Nijariya ta jajantawa Gwamnatin Nasarawa bisa kisan mutani 37 da sojan sukayi kan kuskure

Daga Zubairu Lawal

Babban Kwamandar Rundunar Sojan saman Nijariya Air Marshal Hassan Abubakar ya isa jihar Nasarawa a ranar juma’a 26 ga watan janairun shekara 2024.

Tawagar Sojojin sama karkashin jagirancin Air Marshal Hassan Abubakar ya shedawa Gwamnan Abdullahi Sule makasudin ziyarar shine yiwa Gwamnan da al’umman jihar Nasarawa ta aziyar kisan gillar da Rundunar Sojan sama sukayiwa Fulani makiyaya a kauyen Rukubi a shekarar 2023.

Yace; wannan harin da aka kai yayi sanadiyar mutuwar mutani 37 a kauyen Rukubi dake karamar Hukumar Doma cikin jihar Nasarawa abin tausayawabi.

Sai dai Rundunar tace harin ya faru bisa ga kuskurene, ba da gangan aka tsara wannan harin ba.

Akan hakane tawagar ta iso jihar Nasarawa domin jajantawa al’umman jihar ganin cewa tun lokacin da abin ya faru ake bincike.

Yace: duk da cewa faruwan abin ya kai shekara amma da zafi ace basu ziyarci jihar da abin ya faru sun jajanta ba.

Yace; duk da cewa a lokacin Rundunar Sojan sama NAF ta samu rahotun yan Ta’adda da suka shirya kai hari bisa Babaru. Nan take Rundunar ta dauki matakin dakile harin ta hanyar amfani da jirgi Mara matuki sai ibtila’in ya sauka kan wadannan mutanin.

Gwamna Abdullahi Sule ya jinjinawa Tawagar Sojojin karkashin agorancin Air Marshal Hassan Abubakar dan gane da tattakin da sukayi na zuwa jihar Nasarawa domin ajantawa ga al’umman jihar da kuma iyalan mamatan.

Yace: hakika al’umman jihar Nasarawa dasu ji dadin faruwan haka ba. Kowa ya shiga zulumi a wannan lokacin.

Gwamnatin jihar Nasarawa tayi bakin kokari wajen rarashin iyalan wadanda abin ya faru dasu tsakanin masu rauni da na mamata.

Gwamna Abdullahi Sule ya kuma kara kira ga Air marshal  Hassan Abubakar da su kara kaimi wajen gani tsaro ya inganta a jihar Nasarawa da kasa baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *