Bamu yarda da Kungiyar yan Bangar Fulani a Nasarawa ba
-Inji Kungiyar Matasan Jihar
Daga Zubairu M.Lawal Lafia
Kungiyar matasan jihar Nasarawa bukaci Gwamnatin tarayya data sanya baki domin kawar da Kur ba taceiyar kungiyar yan Banga da Shugaban kungiyar Miyatti Allah na Qasa Alhaji Abdullahi Badejo ya kafa.
Da yake jawabi ga manema labarai a zauren taro na NUJ Shugabar gamayyara kungiyar Matasan Jihar Nasarawa Kwamared Silas Dauda Yileni (President Ethnic Association Nasarawa State).
Yace; “bamu yarda da wannan kungiyar na yan Bangar Fulani a wannan jihar ba”.
Yace; haka kawai da rana tsaka mutani da sutura kala daya sama da mutum dubu daya wai sune za su kare al’umman jihar Nasarawa.
Yace; su masu kare al’umman jihar Nasarawa inane garinsu?. Basu da gari ne ?. Meyasa bazasuje wani jihar ba sai jihar Nasarawa ?. Ya kara da cewa Jihar Nasarawa ba jihar su bane. Kuma waye ya gayyacesu ?.
Yace; suwaye suke hana jama’a zuwa gona? Suwaye suke hana jama’a zama a kauyuka ai kowa ya San fulanine ke garkuwa da mutani a qasan nan.
Kwamared Silas Dauda Yileni yace; sun tattauna da nembobin kungiyarsu daga kowata kabila a jihar Nasarawa kuma kowa ya amince da kuddurin Gwamnati ta kore wannan Kungiyar ta Yan Bangar Fulani a jihar.
Sannan ya kalubalanci Kwamnishinan yan Sandan jihar saboda tarban da yayiwa Shugabanni da membobin kungiyar a lokacin da suka ziyarceshi.
Yace; Jami’an tsarone ke da hakin kare lafiyan al’umman jihar ba wata kungiya da za a kafata rana tsaka, kuma a gansu da Uniform sun cika titi babu izini ba.
Yayi kira ga Shugaban Qasa Bola Ahmad Tinubu da ya dauki wannan kungiyar saboda ire iren haka aka assasa rigingimu dake faruwa a yan kin Arewacin Nijariya da ya hana zaman lafiya.