Yar ‘ Nijeriya ta zama maibaiwa Sakataren MDD shawara

Yar ‘ Nijeriya ta zama maibaiwa Sakataren MDD shawara

Daga Zubairu M Lawal

Sakatare Janar na Majalisar xinkin Duniya Mistar Antonio Guterres ya sanar da bada muqami mai girma ga wata kwarariyar ma’aikaciya yar Nijeriya Misis Joy Ezeilo a matsayin mai bashi shawara ta musamman a bakin aiki.

Ayyukan Misis Joy Ezeilo zai kasance na bada da shawarwari kan abinda ya shafi dukkan ayyukan cigaba Majalisar da kuma shirin bunqasa rayuwar qasashe masu tasowa da alumman da ke cikin kuncin rayuwa.

Misis Joy Ezeilo kwarariyar ma’aikaciyace a vangaren Lauyoyin Nijeriya tana kuma bada gudumawar karantarwa a jami’a a fannin karatun Lauya .

Yanzu ta kasance cikin kwamitin amintattau na Majalisar xinkin Duniya

Kwarewar Misis Ezeilo zata bada gudumawa mai yawa a wanan sashin da aka sanyata kuma zai samar da cigaba Majalisar xinkin Duniya inji Sakataren MDD.

Ya kara da cewa Majalisar xinkin Duniya tana buqatar samar da cigaba masamman a nahiyar Afrka amma dole sai an hada da haziqa yan Afirika saboda alumma su kara fahintar ayyukan cigaba da Majalisar xinkin Duniya ke kawowa yan kunan .

Burinmu samar da tsaro mai dorewa da zai samar da zaman lafiya na dindindin saboda alumma su samu ikon yin walwala a gidajensu.

Ya qara da cewa ; muna ayyukan cigaban gina alumma ta yadda zasu samu abubuwan yi su dogara da kansu. Da shirin nan na rage talauchi a cikin alumma.

Shiyasanya muke koyar da sana’o’in hannu na zamani da harkokin kasuwanci. Masamman ga alumman karkara da kuma wadanda yaqe-yaqe ya lalata rayuwarsu.

Ya kasance sun rabu da danginsu suna rayuwa a wani waje killacece.

Ya kara da cewa; Misis Ezeilo ta samu shiga vangaren kwararo dake taka rawa a Majalisar xinkin Duniya wajen ayyukan cigaba.

Kamar irinsu, Misis Rose Freedman wadda yar qasar Ingila ce.

Sai Mistar Pabio De Greiff daga qasar Colombia, Misis Adrijana Hanusic daga Herzegovina Dakta , Najat Maalla M’jid daga Marocco, Mistar Vitit Muntarbhorn daga qasar Thailand sai Mistar Muna B. Ndulo daga Zambia.

Zasu hada kai domin gudanar da ayyuka na masamman wanda zaikai Majalisar xinkin Duniya ga cimma kudurin da ta sanya agaba na cetowa da bubqasa rayuwar alumma dake cikin kunchi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *