ABIN TAUSAY – Ruwa ya ci kusan mutum 100 a Iraqi

Ruwa ya ci kusan mutum 100 a Iraqi

Daga Aliyu Mustapha

Rahotanni sun ce kusan mutum 100 sun rasa rayukansu bayan da wani jirgin ruwa a kogin Tigris da ke birnin Mosul na kasar Iraqi ya nitse.

Mafi yawancin wadanda ke cikin jirgin ruwan mata ne da yara.

Ministan harkokin gidan kasar ya ce mutane kusan 200 ne ke cikin jirgin wanda ke kan hanyarsa ta zuwa wani wajen tsibiri da ake zuwa domin yawon bude idanu a wani bangare na bukukuwan sabuwar shekararsu.

Hukumar tsaro da ki dauki a Mosul ta ce yawancin wadanda ke cikin jirgin ruwan ba su iya ruwa ba.

Akalla akwai yara 19 da mata 61 daga cikin wadanda aka rawaito sun rasa rayukansu sakamakon nitsewar jirgin, yayin da aka ceto asu mutum 55.

Mutanen dai na kan hanyarsu ta zuwa tsibirin Umm Rabaen wanda ke da nisan kilomita 4 daga arewacin birnin Mosul inda za su je domin bikin sabuwar shekararsu ta Nowruz.

 

Wasu hotunan wajen da aka dauka sun nuna jirgin ya jirkice gefen dama ruwa na ta shiga cikinsa kafin ya kife gaba daya, sannan kuma ruwan kogin da ke gudana da yawa ya nitsar dashi.

Kazalika wasu hotunan wajen sun nuna yadda mutane ke yawo a kan ruwa.

Wani ganau ya shaida wa kamfanin dillancin labari na AFP cewa, jirgin ruwan ya dauki fasinjoji da yawa hakan ya sa saboda nauyi ruwa ya fara shiga cikinsa.

Shi ma wani ganau din ya ce da idanuwansa ya ga gawar yara a saman ruwan.

Tuni dai motocin daukar marassa lafiya da jirage masu saukar ungulu suka isa wajen domin aikin ceto da kuma neman gawar wadanda suka mutu a cikin ruwan.

 

Dama dai mahukunta na yi wa jama’a gargadin a kan cewa kogin zai tumbatsa da ruwa saboda bude madatsar ruwa ta Mosul, lamarin da ya a wasu mutane suka zargi matukin jirgin da watsi da wannan shawara.

Fira ministan kasar Adel Abdul Mahdi, ya bayar da umarnin gaggauta bincike a kan musabbabin afkuwar lamarin.

Kazalika Fira Ministan ya ce, bayan samun labarin afkuwar wannan lamari y tausayawa wadanda lamarin ya rutsa da su, sannan kuma ya ce a gaggauta ceto wadanda ke da rai domin kai su asibiti don a yi musu magani.

Mr Mahdi, ya kuma kai ziyara asibitin da aka kai mutanen domin duba su, da kuma ziyartar dakin ajiye gawawwaki, sannan kuma ya ayyana zaman makoki na kwana uku a fadin kasar.

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *