Kowa zai karbi magani kyauta a Asibiti – Gwamnatin Nasarawa
Daga Zubairu M. Lawal
Gwamnatin jihar Nasarawa tayi kira ga alumman jihar cewa kowa zai iya zuwa Asibiti mafi kusa domin karbar magani na cutar dake daminsa.
Da take jawabi ga manema labarai Kwamishiniyar kiwon lafiya ta jihar Nasarawa Dakta Roseline Kela tace ranar 7 ga watan afirilu shine ranar da aka ware domin bikin ranar lafiya ta Duniya.
Saboda haka tuni Gwamnatin jihar Nasarawa ta tanadi magunguna wanda zata baiwa duk wanda ya haralci Asibitin dake kusa dashi.
Tace: duk shekara ake gudanar da wanan shiri kuma mutum koyana da lafiya ko bai da lafiya ana bukatar ya shiga kowani Asibiti domin duba lafiyan jikinsa.
Tace akwai Hukumar kiwon lafiya ta inshora wanda Gwamnati da masu fada aji zasu zuba jali domin a bubkasa harkan kiwon lafiya da zai taimaki talakawa.
Ta kara da cewa yanzu Gwamnatin jihar Nasarawa ta dauki ma’aikatan sakai kimanin 600 da zasu rika taimakawa suna fadakar da alumman unguwanni da karkara mahimmancin zuwa Asibiti idan mutum bashi da lafiya ko masu haihuwa maimakon suyi ta zama a gida cuta na daminsu za’ataimaka masu su zo Asibiti.
Kuma ma’aikatane na aikin gaggawa da zasu fadakar su kuma nunawa alumma yadda zasuyi koda cutar kwalara ya billo a gari .