Nijeriya da M.D.D sun kulla yarjejeniya kan yada labarai

Nijeriya da M.D.D sun kulla yarjejeniya kan yada labarai

Daga Zubairu M Lawal

Gwamnatin Tarayyan Nijeriya da Majalisar Dinkin Duniya sun kulla yarjejeniyar harkokin yada labarai da harkokin cigaba mai daurewa.
Kuddurin zai cigaba har zuwa tsawan shekarar 2030. Mai baiwa Shugaban kasa shawara kan harkokin bunkasa rayuwar karkara da shir na musamman .

Misis H. E. Princess Adejoke -Adefulire Da Mataimakiyar Sakataren Majalisar Dinkin Duniya  Hajiya Amina Garba aka tsaida wanan yarjejeniyar a tsakanin bangarori biyu a birnin New York dake kasar Amurka a taron kafafen yada labarai da ya gudana acan.

Yarjejeniyar zai maida hankaline wajen fadakar da wayar dakan alumma saboda su fahinci kudurorin cigaba da Majalisar Dinkin Duniya ke gabatarwa domin cigaban alumman kasar.

Kafafen yada labarai zasu rika nuna  ire-iren abubuwan cigaba mai amfani masamman wadanda ake samarwa ga yan gudun hijira da alumman karkara marasa galihu.

Kuma za’a rika wayar dakan alumma yadda zasu fahinci harkokin , da yadda zasu rika mu’amala da juna . da zaman lafiya, da baiwa ma’aikatan  Majalisar Xinkin Duniya hadin kai a duk lokacin da suke gudanar da wasu shirye- shirye na cigaba cikin alumma.

Za’ayi amfani da Fina finai na wasan kwaikwayo ana nunawa a gidajen Talabijin da sanyawa a rediyo da yanar gizo da sauransu ta yadda zai kara wayar dakan alumma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *