Daktan Talakawa ya ceto rayuwar ya’yanmu kyauta – Iya’yen Yara
Daga Zubairu M Lawal
A cigaba da ayyukan Gidauniyaw Doctor on the Africa wanda Likitan Talakawa Honorabul Joseph Haruna Kigbu ke jagoranta, yana samun adu’a da sanya albarka a bakin dubbannin alumma.
A baya bayan nan tawagar ta sauka a garin B.A.D. dake karamar hukumar Lafia dake jihar Nasarawa a ranar alhamis 4/4/2019.
Dubban alumma maza da mata da yara kanana suka samu halartan wanan gurin domin samun magani ko Tiyata kwayta .
Bayan dogon layi na karban kati mutani sunci gaba da zuwa ganin Likitochin da suke gudanar da ayyuka a vangarori dabam dabam.
A ranar Juma’a Wakilinmu ya kasance a gurin ya samu zantawa da wasu bayin Allah da laluran rashin lafiya yake daminsu amma babu kudin zuwa Asibiti.
Sunanan Abdullahi Sule na dade ina fama da lalurar idanu duka idanuwana basu gani nayi jigilar zuwa Asibiti akace sai naje Asibitin IDO a Kaduna nikuma bani da karfin zuwa Kaduna.
Na kasance tsawan shekaru ina zaune bana gani yarana ke taimakawa suna jana zuwa waje su dawo dani.
Yanzu gashi anyimin aiki a Idanuna kyauta yanzu ina gani sosai. Bani da abinda zancema wanan bawan Allah saidai muyi masa Adu’a Allah ya saka masa da mafi kyawun alheri.
Samuwel Agun yace; yanzu ina gani sosai kamar yaro karami. Adu’a kadai zamuyima Likitan Talakawa duk abinda yake nima Allah ya bashi.
Sunanan Lidiya Goudwing John yarona ya dade yana fama da wanan cutar a mararsa tun yana karami amma bamu da kudin zuwa Asibiti yanzu Allah ya kawo Honorabul Joseph Haruna Kigbu fitar damu daga wanan matsalar . Fatana Allah yayi masa albarka shida tawagarsa baki daya .
Hajara Nuhu yarana guda biyu gasucan anyi masu Tiyata an kuma bamu magunguna . Muna adu’a Allah ya sakama Likitan Talakawa da alheri.
Bala Audu anyiwa matata aiki kyauta mutafi Asibiti an yanka mana kudi mai yawa tun shekara biyu da rabi mun kasa biyan kudin da za’a yi mata aiki.
Amma Allah da ikonsa yanzu gata a kwance a gado anyi aikin kuma an bamu magani kyauta. Nima ina fama da kafa an dubani an bani magani. Kuma matsalar IDO an dubani ance idona ba sai anyi Toyata ba an bani Madubi ina gani.
Zamuci gaba dayi masa adu’a Allah ya kareshi ya kara matsa tsawan kwana tare da mutaninshi.
Maryam Ibrahim sunana, Allah yasakama Dakta Joseph Haruna Kigbu da alheri yarona yana fama da cutar mara kuma bamu iya barci idan ya taso masa , muna son muje Asibitin Keffi ko Abuja amma gashi da maigidana ya kawomu , anyima yaron Tiyata kwata kuma ambashi magani .
Shima mai gidana an bashi maganin hawan jini . Muna masa fatan alheri kamar yadda yake taimakawa talakawa shima Allah ya taimakeshi a dukkan lamarinshi.
Sunana Dauda , ni nazone na gani amma ni banzo da mara lafiya ba kuma ni Lafiya na kalau. Amma muna masa fatan alheri, saboda abinda nagani yakeyi na taimakawa alumman kasan nan bamuda abinda zamuce masa saidai Allah ya saka masa da alheri.
Ya kara da cewa da yan siyasa zasu irkayin haka wallahi da babu mai zaginsu a kasan nan. Wanan bawan Allah abinda yakeyi na cigaban alumman kasa ,yafi abinda Gwamnati keyi.
Saboda kaba mutum lafiya yafi kabashi kudi ko ka gina hanya. Saboda sai da lafiya ake tafiya . kuma sai da lafiya ake jin dadin kudi.
Duk yan siyasan mu na Jihar Nasarawa kai dama Arewa ta tsakiya da Arewacin Nijeriya baki daya da ace zasu rika gudanar da ayyuka kamar yadda Honorabul Joseph Haruna Kigbu keyi da yanzu bamu da Matsala a Arewa.
Kigbu yana gudanar da ayyukan shi ga kowa da kowa baya duba waye kai mai kudine ko talaka, mai mulkine ko mai Sarauta, Musulmi ne ko Kirista, baya wanan kaga haka akeson mutum wanan shine mutum na gari .
Mutumin kirki mai taimakawa alumma mai son cigaban alumma .
Na zaga naga yadda Ma’aikatansa sukeyi da Jama’a cikin saukin kai . Na shiga dakin da yake duba marasa lafiya mun gaisa dashi naga yadda yake karban marasa lafiya babu kyamatar mutani.
A garin na B.A.D dai dubannin alumma ne suka amfana da wanan tallafin na Gidauniyar Doctor on the Mover Africa wanda ya gudana tsawan yini uku. Alhamis Juma’a Asabar.