Samar da kaykayawar muhalli zan kawar da cututuka a Nijeriya

Samar da kaykayawar muhalli zan kawar da cututuka a Nijeriya

Inji Antonio Guterres

Daga Zubairu M Lawal

Sakatare Janar na Majalisar Xinkin Duniya Mister Antonio Guterres yayi kira da a samar  da kyakyawar muhalli mai mahimmanci ga alumma.

Sakataren Majalisar Xinkin Duniya ya nime goyon bayan Gwamnatochi da masu fada aji da su taimakawa unguwannin marasa galihu dake fama da mummunar yanayi, da gurbatacen muhalli dake janyo cututuka kamar kwalara da zazzabin cizon sauro.

Sakataren yayi wanan kirane a taron ranar tsaftar muhalli ta Duniya da ya gudana a ranar 30 ga watan uku na wanan shekarar.

Yace; tsaftar muhalli abune mai mahimmanci ga rayuwar alumma.
Yace; gidaje da unguwanni suna da buqatar samun tsafta saboda yana taimakawa rayuwar alumma. Tsafta abune mai mahimmanci, amma rashin tsaftace gurare yana haifar da damuwa da cututuka.
Yace; gari irin  Abuja Babban birni yana buqatar tsaftacece gurare ko da yaushe.
Baya bukatar kazanta  ko cunkoson da zai riqa haifar da rashin tsafta .

Kuma rashin tsafta yana haifar da mummunar yanayi, Sakataren ya qara da cewa; abinda ya kamata Hukuma ta qara wayar dakan alumma su fahinci mahimmanci tsaftace guraren zamansu .

Da makwancinsu da yanayin ruwansha mai tsafta da tsaftace guraren dafa  abinchi da guraren wasannin yara.

Yace; miliyoyin Jama’a ne ke zama a Babban birnin amma akwai qarancin abubuwan tsaftace muhalli na zamani. Wanda yana da amfani ga rayuwar alumma qasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *