Shirye nake na kalubalanci Ali Nuhu a gaban kotu – Adam Zango
Daga Madina Ibrahim
Sabon rikicin da ya barke tsakanin manyan Jaruman Fina-Finan Hausa a Nijeriya ya dauki sabon salo a tannin Shari’a. Bayan Babban Jarumi Ali Nuhu ya maka abokin sana’ansa Adam Zango gaban kotu a ranar alhamis.
Adam Zango yayi magana a kan rikicinasa da Ali Nuhu
Yace sam bai yi nadamar fitowa ya kare Mahaifiyarsa ba .Yanzu haka za a shiga kotu tsakanin manyan Taurarin guda biyu dake da dubbin magoya bayan a ciki da wajen Industry.
Idan ba ku manta ba a Ranar Alhamis, 11 ga Watan Afrilun 2019 ne aka shigar da karara babban ‘Dan wasa Adam A Zango a gaban kotu. Ba kowa bane ya kai wannan Tauraro kara face Takwaran sa watau Ali Nuhu.
Bayan Adam Zango ya ji labarin wannan sammaci, ya fito shafin sa na Facebook ya godewa Ubangiji na samun damar wanke kan sa. Kotu dai ta nemi Fitaccen ‘dan wasan ya zo kare kan sa daga tuhumar da ake yi masa.
Babban ‘Dan wasan ya nuna cewa a shirya yake da ya halarci zaman kotun da za ayi inda yake cewa Allah ya nuna masa zuwan wannan rana. Tauraron ya kara da cewa sam bai yi da na sanin fitowa ya kare Mahaifiyarsa ba.
Alhaji Adam Zango a jawabin na sa yake cewa ba zai bari a ci mutuncin Mahaifiyarsa yana ji yana gani ba. Zango a karshen jawabin na sa yake cewa ko me zai faru da shi a dalilin kokarin kare martabar uwarsa, ba zai damu ba.
A cikin ‘yan kwanakin nan ne Adam Zango yake zargin cewa Ali nuhu ya tunzura Yaransa su ci masa mutunci, wannan ya sa shi ma ya fito ya maida a gaban Duniya a kafafen sadarwa na zamani