Jama’a na amfana da taimakon Dr. Kigbu a jihar Plateau
Daga Zubairu M Lawal
Dubban alumma suna amfana da Gidauniyar Kwararun Likitochin Afirika wanda suke kula da harkokin kiwon lafiya yin Tiyata da bada magani kyauta .
Bayan tawagar Kwararun Likitochin Afirika wanda Kwararen Likitananan na jihar Nasarawa Hon.Joseph Haruna Kigbu ke jagoranta , ta baro jihar Bauchi inda ta gudanar da aiki na tsawan kwana shida . a shirin tallafin kiwon lafiya na mutum 10,000 Wanda kakakin Majalisar wakilai ta tarayya Hon. Yakubu Dogara ya dauki nauyi aka gabatar a Asibitin Abubakar Tafawa Balewa dake Bauchi da Asibitin Gwamnatin tarayya dake Azare.
Yanzu haka dai tawagar ta kama aiki gadan gadan a jiyar Plateau tun a ranar Alhamis 2/5/2019 inda zasuyi kwanan uku.
Yanzu aikin kiwon lafiya na gudana a Babban Asibitin Bagwaro da kuma Babban Asibitin Shandan dake kudancin jihar Plateau.
Dubban alumma suke tururuwa zuwa bayyana damuwar cututukar dake daminsu domin samun Tiyata da magani kyauta.
Tawagar Gidauniyar Kwararun Likitochin Afirika suna gudanar da manya manyan Tiyata na cutar dake makale a jikin mutum masamman mata masu fama da cuta a mahaifa da sauransu.
Maza da mata manyan da yara suna kaiwa da komowa domin niman waraka.
Jagoran tafiyar Hon. Joseph Haruna Kigbu wanda akewa lakabi da Likitan Talakawa ya kasance dashi ake gudanar da wanan aiki.
Babu kama hannun yaro .
Alumma suna godiya da sa’albarka. Kowa kajishi adu’a kawai yakeyiwa wanan tawagar likitan Talakawa.
Shirin da yake gudana a jihar Plateau ya kasance hadin giwane ga Asibitin jami’ar Gwamnatin tarayya dake garin JOS . ( JUTH)