Nasarata a kotu cigabane ga alumman Nasarawa ta kudu
Inji Sanata Al-makura
Daga Zubairu M Lawal
Tsohon Gwamnan jihar Nasarawa kuma Sanata maichi ya bayyana cewa nasarar da ya samu a koton qarar zabe wanda Sanata Solomon Asenya Adekwe na jam’iyyar PDP ya kaishi tankar cigabace ga alumman Nasarawa ta kudu.
Yace; duk da rashin amsar sakamakon zaven da Dan takarar PDP yayi a wancan lokacin ya kuma qalubalanci sakamakon a gaban kuliya to alumman yankin Nasarawa ta kudu sunyi ruwa sunyi tsaki sunga cewa wanda suka zaben shine yayi nasara a gaban shari’a.
Sanata Al-makura yace; rashin godiyar Allah ne ya sanya Dan takarar PDP zuwa kotu.
Yace; gashi wanda yakai qarar ya kasa tabbatarwa kotu hujoji da zargin da sukayi.
Yace; sun kyele mutum daya wanda shima bai iya tabbatarwa kotu gaskiyar abinda suke zargi ba.
Ya kumace ; Lauyoyina da sheduna sun gansar da kotu irin hujojin da muke dashi nayin nasara da zunzurutun kuri’u.
Sanata Umar Tanko Al-makura ya qara da cewa munji cewa zasu daukaka qara to dama wanan kundin tsarin dokokin qasa yaba kowani xan qasa damar idan akayi masa ba daidai ba ya dauka ka qara .
“Amma ina mai tabbatar maku koda ya daukaka qara lauyoyinmu da shedunmu sunana kuma zasubi ko ina su tabbatar da cewa hukuncin da akayi a nan na nasarar da muka samu shine zamu sake samu a gaba”.
Yace qara da cewa yadda Jama’a suka zaven saboda nayi masu ayyukan alheri to bazan sauya ba ,kuma zan tabbatar nayi masu abubuwan da zai amfanesu.