KOTU TA YANKEWA RASHIDA HUKUNCIN KISA BAYAN TA SAME TA DA LAIFIN KASHI MIJINTA
Daga Aminu Musa
Wata babbar kotun jihar Kano a ranar Jumaa ta yankewa wata mata mai suna Rashida Saidu hukuncin kisa ta hanyar rataya kan laifin kisan mijinta, Adamu Ali, ta hanyar turoshi daga gidan tsauni a jihar.
An shigar da Rashida kara kotu ne a shekarar 2019 kan zargin ta da hannu cikin kisar mijinta wanda ya kasance ma’aikaci a kwalejin ilimin tarayya FCE Kano.
Lauyan gwamnati Mariam Jibrin, ta bayyana wa kotu cewa Rashida ta samu sabani da mijinta ne a gidansu dake unguwar Dorayi kimanin shekara daya da ta gabata.
Ta kara da cewa yayinda suka fara fada, sai ta turoshi kasa daga gidan tsauni kuma hakan yayi sanadiyar mutuwarsa.
Yayinda ake shari’ar, an gabatar da shaidu hudu a kotun domin bayar da shaida kan tuhumar da ake mata.
Amma Rashida ta bakin lauyanta, Iliya Dauda, ta musanta zargin kuma ya gabatar da nata shaidun.
Bayan kwashe watanni ana shari’a, an yankewa Rashidah da ta kashe mijinta a Kano hukuncin kisa