Adewale Wally Adeyemo: Ɗan Najeriyar da Biden ya bai wa mataimakin ma’ajin baitil malin Amurka

Adewale Wally Adeyemo: Ɗan Najeriyar da Biden ya bai wa mataimakin ma’ajin baitil malin Amurka

Wani lauya haifaffen Najeriya kuma tsohon babban mai bai wa shugaban Amurka Barack Obama shawara kan tattalin arzikin duniya, Adewale Adeyemo, zai zama sabon mataimakin ma’ajin baitil malin Amurka, a cewar kafofin yaɗa labaran ƙasar.

Adeyemo zai yi aiki ne tare da Janet Yellen, bayan da zaɓaɓɓen Shugaba Joe Biden ya zaɓe su a matsayin ma’aji da mataimakin baitil malin ƙasar.

Muƙamin Adeyemo na ɗaya daga cikin muƙaman da ake sa ran Biden zai sanar da su nan ba da jimawa ba.

Wane ne Adewale Adeyemo?

An haifi Adewale Adeyemo da aka fi sani da “Wally” a shekarar 1981 a Najeriya, amma ya girma a California.

Ya yi karatunsa na digiri a Jami’ar California kafin daga bisani ya tafi makarantar Koyon Shari’a ta Yale.

Kafin ya fara aiki a ƙarƙashin mulkin Oba,a, Adeyemo ya fara aiki ne a matsayin edita a a wani shirin bunƙasa tattalin arziƙi na Hamilton Project, sannan ya yi aiki a matsayin babban mai ba da shawara da kuma mataimakin shugaban ma’aikata na Jack Lew a baitil malin Amurka.

Daga bisani ya yi aiki a matsayin mai sasantawa na yarjejeniyar kasuwanci ta ƙasasehn duniya 12 ta Trans-Pacific Partnership, sannan shi ne shugaban ma’aikata na farko a hukumar Consumer Financial Protection Bureau ƙarƙashin jagorancin Elizabeth Warren.

A shekarar 2015, an naɗa shi a matsayin mataimakin mai ba da shawara kan tsaro na ƙasa a harkokin tattalin arzikin ƙasashen duniya da kuma mataimakin darakta na Cibiyar Tattalin Arziki ta ƙasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *