Majalisar Dinkin Duniya sun hada hannu da Gwamnati wajen raba abinci
Daga Zubairu M Lawal
Gwamnatin Najeriya da majalisar Dinkin Duniya, sun hada hannu wajen taimakama yan Najeriya da kudade da kuma abinci domin rage radadin talauci da annobar cutar Korona ya haifar.
Hukumar rabon kayan taimakon tace anyi la’akari da yanayin da wasu jihohi a Nijeriya suka tsince Kansu saboda iftila’in da ya addabe jihohin a lokacin cutar Korona Bairus
taimakon dai zai shafi, Babban birnin tarayya Abuja da jihar Kano da kuma jihar Legas manyan biranen kasuwanci da yawan jama’a.
Taimakon dai ya biyo bayan irin barnar da cutatar Korona Bairus tayi wa al’umman dake gudanar da harkoki a jihohin da ma Gwamnatin jihar.
Gwamnatin Najeriyan dai ta saki Ton 2,000 na abinci, wanda kudin su ya kai dalan Amurka Miliyon Daya, sai kuma dala Miliyon Uku da ta bada domin tallafawa Al’umma a wadannan jihohin.
Sannan Majalisar Dinkin Duniya ta saki tallafin abinci da kudaden da yawan su yakai Dalan Amurka miliyon uku.
Tace wannan tallafin zai ragewa jama’an jihar radadin da ya samesu a lokacin annobar cutar Korona Wanda ya sanya dadamar mutani sun durkushe har yanzu sun kasa farfadowa.
Za a yi rabon ne bisa la’akari da yawan jama’a dake dukkanin jihohin. Za a kuma duba yana yin da kowata jihar ta shiga na matsalar rayuwa a wannan lokacin.
Kuma kowata jihar ba za a barta da kanta ba wajen rabon agajin da za a bada. Dole zai kasance da kulawar hukumar kula da rabon kayan agaji da Ma’aikatan walwala ta Nijeriya da kafafen yada labarai.