MATAKAN TSARO – AN KADDAMAR DA RUNDUNAR YAN SANDAN JIHAR NASARAWA

AN KADDAMAR DA RUNDUNAR YAN SANDAN JIHAR NASARAWA

Daga Zubairu M Lawal

Gwamnatin jihar Nasarawa ta rantsar da Rundunar hadin giwa na yan sandan cikin al’umma kimanin 503, da zasu aiki kafada da kafada da Rundunar yan Sandan kasa a fadin jihar.

Da yake jawabi Gwamnan jihar Nasarawa wanda ya samu wakilcin Mataimakin Gwamnan jihar Dakta Emmanuel Akabe ya bayyana jin dadinsa da samar da wannan Rundunar da zasu taimakawa Rundunar yan Sanda aiki a cikin al’umma

Ya shawarci wadanda aka dauka aikin da suyi aiki gaskiya da gaskiya domin kare martaban jihar Nasarawa.

Ya kuma ce Gwamnatin jihar Nasarawa zata cigaba da samar da duk abinda Rundunar yan Sandan jihar ke bukatar domin kare rayuka da dukiyoyin al’umman jihar.

Shima Mataimakin Sufeto Janar na Rundunar yan Sandan Nijeriya shiyar Arewa ta tsakiya dake zaune a garin Makurdi ta Jihar Benue Mista Jona John ya ce tsaron rayuka da dukiyar al’umma hakine da ya rataya a kan kowa da kowa, Kuma  kowa na da rawar da zai taka wajen tabbatar da zaman lafiyan kasan nan.

Shima Kwamishinan yan Sandan jihar Nasarawa Mista Bola E.Longe ya bayyana kwamitin yan Sandan hadin giwar a matsayin babban nasara da za a samu wajen kawar da bata gari.

Ya ce , zasu taimakawa yan Sanda wajen bayyana masu laifi dake buya a cikin al’umma,

Ya ce Rundunar yan Sandan jihar Nasarawa zata bude kunnen ta wajen sauraron bayanai ta ko ina domin kawar da bata gari dake addabar al’umman jihar.

Rundunar yan Sandan farin kaya ta hadin giwar sun samu horo a sashin gudanar da koyon aiki na Rundunar yan Sandan kasa dake garin Makurdi cikin jihar Benue.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *