HAJIYA SILIFAT A.A.SULE TA KARRAMA YAN SANDAN DAKE AIKI TARE DA ITA

A ranar Laraba Giwan Matan Jihar Nasarawa Kuma Shugaban Matan jihar Uwargidan Gwamna Abdullah Sule Hajiya Silifat ta karrama Rundunar yan Sandan dake aiki a ofishin ta.

Karramawar da tayi masu ya biyo bayan kwazon da bajintar da suke aikatawa a bakin aiki.ta Kuma yaba masu kan yadda suke gudanar da aiki tare da nuna kwarewa.

Hajiya Silifat wanda ta rika samun yabo daga sasa dabam dabam na fadin kasan nan . saboda yadda take taimakawa marasa galihu da yaki da masu cin zarafin mata da yara kanana.

Saboda wannan kwazon nata da kyautatawa ya sanya masarautar Lafia dake babban birnin jihar Nasarawa ta karramata da sarautar Giwan matan jihar Nasarawa,

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *