ZA A SHA KALLO – Yadda gasar bukin nuna tsaraici zai kasan ce a garin kaduna za a yi yawo tsirara

A SHA KALLO –  Yadda gasar nuna tsaraici na SEX PART: zai kasance a Kaduna za a yi tafi tsirara.

Ƴan sanda a Kaduna sun damƙe wasu matasa da suka yi niyyar haɗa wata dabdala ta nuna tsiraici wadda aka yi ta tallatawa a shadfukan sada zumunta baya-bayan nan.

An yi niyyar yin wannan dabdalar a ranar 27 ga watan Disamban 2020 kafin gwamnatin jihar Kaduna ta daƙile yunƙurin matasan.

Waɗanda suka shirya wannan dabdalar, sun buƙaci mahalarta bikin su je wurin tsirara.

Mai taimaka wa gwamnatin jihar Kaduna kan kafofin watsa labarai, Abdallah Yunus Abdallah ne ya tabbatar wa BBC da batun kama waɗanda suka yi niyyar shirya wannan ƙwarya-ƙwaryar bikin.

“Lambar da suka saka kan takardar gayyata, ita aka yi amfani wurin gano waɗanda suka shirya dabdalar kuma a yanzu an kama su,” in ji shi.

Wannan shi ne karo na farko da aka yi yunƙurin gudanar da irin wannan dabdalar a bayyane a arewacin Najeriya.

Mai magana da yawun ƴan sanda reshen jihar Kaduna, ASP Mohammed Jagile ya tabbatar wa BBC da wannan lamarin inda ya ce daga nan gaba kaɗan zai yi ƙarin bayani a kai.

Me mutane ke cewa kan wannan dabdalar?

Batun wannan dabdalar ya zama ɗaya daga cikin abubuwan da aka rinƙa tattaunawa a ƴan kwanakin nan musamman a shafukan sada zumunta.

Mutane da dama sun yi zaton batun wannan dabdalar wasa ne kawai, ko kuma irin tsokana ce da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta, sai da suka ji labarin cewa gwamnatin jihar ta kama waɗanda suka shirya bikin tukuna suka yarda da gaske ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *