MATASA ZASUYI FARIN CIKI A NASARAWA Gwamna Abdullah Sule ya rattaba hannu kan kasafin kudin 2021

AL’UMMAN JIHAR NASARAWA ZASUYI BAN KWANA DA TALAUCI – bayan  Gwamna Abdullah Sule ya rattaba hannu kan kasafin kudin 2021

Daga Zubairu M Lawal

Gwamna Abdullah Sule na jihar Nasarawa ya rattaba hannu kan kasafin kudin shekarar 2021 a ranar Laraba 30/12/2020.

ya rattaba hanu Kan kasafin kudi’ adadin N112,923,174,543 Wanda Majalisar Dokokin jihar sukayi aiki akai na shekarar 2021 ya Zama doka.

A lokacin taron rattaba hanun wadda yagudana a dakin taro na Gidan Gwamnati, dake garin Lafia.

Gwamnan yace za a  aiwatar da duk abunda ke cikin Wanann kasafi dayasa a hannu a yau doka ne ta Shekarar 2021.

Gwamnna Abdullah Sule ya bayyana cewa, Kasafin Kudin 2021 yafi wadda akayi na 2020 yawa, yace an shirya hakane don Gwamantinsa tasamu damar dai-daita abubuwar da aka cimma musamman  Samar da abubuwar more rayuwa wa al’ummar jihar Nasarawa.

Samar da manyan ayyuka da kammala wadanda suke a kasa da gyara tattalin arzikin jihar da abubuwan jin dadi ga al’umman jihar da zasu amfana da romon Damukurdiyya.

Gwamnatin jiha zatayi dubi a duka bangarorin Gwamnati don tabbatar da cewa kowani fanni anyi irin ayyukan da aka shirya.

Ya kuma Kara dacewa, Gwamantin jiha zata bunkasa da Samar da ayyuka a duka lungu da sako na jihar, bun kasa harkan noma ilumi zaman lafiya, kiwon lafiya da sauransu. dakuma sa idon yan’ Majalisu don tabbatar da adalci da Gaskiya.

” Gwamnan ya yi godiya ga yan Membobin Majalisar Dokoki na jihar da Shugaban Majalisan Balarabe Abdullahi saboda yadda suka dage  tukuru wajen ganin an duba kasafin suka Kuma yi kyakyawar aiki akai.

Gwamnan ya yi godeya ga banagaran zartarwa a cikin kankanin lokaci da sukayi aiki Akan kasafin kudi’n wadda ayau nake rattaba hannu ya zama doka.

Shugaban masu rinjaye na Majalisar Hon. Umar Tanko Tunga wanda ya wakilce Kakakin Majalisar jiha wadda shi ya jagoranci tawagar Manyan Jami’an Majalisar Dokoki don mika wa Maigirma Gwamna  Abdullah Sule kasafin Saboda ya zama doka, muna da tsammanin aiwatar da wannan kasafi don Samar da abubuwar more rayuwa wa al’ummah.

Maigirma Gwamna, munzo ne a yau mu mika maka kasafin kudi’n don yazama doka kamar yadda doka yatanadar a cikin kundin tsarin mulki na 1999.

” A lokacin da Majalisar Dokoki ta karbi kasafin kudi,ta dakatar da duk wasu ayyuka su
Muka dukufa ka’in da na’in wajen anyi  aiki akan kasafin don tabbatar dacewa munyi shi Akan lokaci.

Yazama dole a dai-dai wannan lokaci inyaba da hadinkai da goyon baya da hukumomin Gwamnati suka bamu musamman Ma’aikatan kasafi da tsare-tsare wadda munsamu munyi aiki dasu akan lokaci har aka kai wannan
lokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *