KU KUNSAN – Sakamakon yaki kamfanonin jiragen sama sun dakatar da sauka da tashi a kasar a kasar isra’ila

Sakamakon yaki kamfanonin jiragen sama sun dakatar da sauka da tashi a kasar a kasar isra’ila

Daga Amina Sani

Rikici tsakanin kasar Isra’ila da Falasdin ya tilastawa kamfanonin jiragen sama dakatar da zuwa kasar Yahudawan yayinda ake kira ga kasashen duniya su sanya baki.

A cewar AFP, Kawo ranar Alhamis, akalla kamfanonin jiragen kasashe bakwai sun sanar da cewa jiragensu zasu daina zuwa Isra’ila.

Kamfanin KLM na kasar Holland ya dakatar da zuwa Isra’ila a yanzu, tashar NOS ta bayyana.

Shi ma Kamfanin kasar Birtaniya ya dakatad da dukkan jiragen da suka shirya zuwa Tel Aviv ranar Alhamis, hakazalika kamfanin Virgiin Atlantic ranar Alhamis a Juma’a.

Kamfanin Lufthansa na kasar Jamus ya sanar da cewa muna sa ran komawa tashi zuwa Isra’ila ranar Asabar, 15 ga Mayu.”

Kamfanin jirgin na kasar Spain ya fasa tafiyar da yayi niyya zuwa Isra’ila na ranar Alhamis da kuma Asabar.

Wata mai magana da yawin Iberia ta bayyanawa AFP cewa ” Zamu yanke shawara kan yadda abubuwa zasu kasance dangane da yadda abubuwa suka kasance.”

Shi ma Kamfanonin jiragen Amurka akalla 3; United, Delta da American Air sun dakatar da jiragensu daga zuwa Isra’ila.

Sai LOT! Kamfanin jirgin na kasar Poland ya “dakatar da zuwa Isra’ila a yanzu”. Kakakin kamfanin Krzysztof Moczulski ya ce: “Ina tunanin ba zamu je na da wasu kwanaki ba.”

Kungiyar kare mutumcin kasar Falastinu wato Hama’s ta sanar da harba makaman Roka guda 250 zuwa Babban birnin Tel Aviv da wasu manyan biranai inda suka tabbatar da makaman sun sauka a filin jiragen saman Tel Aviv.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *