Manchester City ta cimma yarjeniyar daukar Erling Haaland

Manchester City ta cimma yarjeniyar daukar Erling Haaland

Manchester City ta cimma yarjejeniyar daukar dan kwallon tawagar Norway, Erling Haaland daga Borussia Dorrtmund.

Haaland mai shekara 21, zai koma City a watan Yuli, bayan da za ta biya kunshin kwantiraginsa ta fam miliyan 51.2, kudin da aka gindaya idan zai bar Dortmund wa’adinsa bai cika ba.

Wannan cinikin ya bai wa City damar maye gurbin Sergio Aguero, wanda ya koma Barcelona a bara.

Ranar Litinin likitoci suka kammala auna koshin lafiyar Haaland a Belgium, bayan da kungiyar da ke buga Bundesliga ba bashi izinin zuwa can.

Dan wasan ya ci kwallo 88 a karawar da ya yi wa Dortmund tun bayan da ya koma kungiyar daga Red Bull Salzburg a Januarun 2020.

Real Madrid da Barcelona dun sun tattauna da Haalnd kan batun daukarsa, amma ya zabi zuwa Etihad da taka leda

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *