WATA SABUWA, NASARAWA: Ina tare da duk Dan takarar APC a Nasarawa

Ina tare da duk Dan takarar APC a Nasarawa
Inji Al-makura
Sanata mai wakiltan Nasarawa ta kudu a majalisan Dattijai Sanata Umar Tanko Al-makura ya bayyana haka wajen kaddamar da tawagar yakin niman zabensa karo na biyu.
Al-makura yace yana tare da dukkanin yan takarar APC daga muqamin Shugaban kasa zuwa Gwamna da majalisan Dattawa da na Wakilai dama yan majalisan dokoki  ta jihar.
Al-makura yace; al’umman jihar Nasarawa sun bamu goyon baya a lokacin da muka fito takarar niman Gwamna, lokacin bamu da kujerar koda kansila.
Mun samu goyon bayanan al’umman jihar mukayi nasara a shekara ta 2011. Sai da muka kafa Gwamnati na shekara 8.
Ayyukan alheri da mukayi a fadin jihar ya sanya a shekarar 2019 da Gawamna Abdullahi Sule ya fito daga jam’iyyar APC bamu sha wahala ba wajen tallatashi.
Sanata Al-makura yayi kira ga ya’yan jam’iyyar APC dasu fito kwai da kwarkwata su tabbatar sun zabe yan takarar APC daga sama har kasa.
Yace; Gwannatin APC ta A.A.Sule ta gudanar da dumbin ayyukan alheri a Nasarawa.
Saboda haka bazaiyi wahala wajen tallata APC da yan takararta a fadin jihar Nasarawa ba.
Al-makura yace; “Kamar yadda mukayi ayyukan cigaba a matsayin Sanata muna da kwarin giwan samun goyon bayanku a karo na 2”.
Andai kaddamar da mukamai hudu cikin 200.
Jagorar yakin niman zaben Alhaji Umaru Sulaiman Azoz.
Mataimakinsa Hon. Adamu Sule
Sai mai bada shawarwari na musamman  Edward Auta
Sakataren kwamitin Hon.Nasiru Abdullahi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *