2023 zamu sharewa Gwamna Sule hawaye a Nasarawa
Inji Aminu Maifata
Daga Zubairu Lawal
Shugaban Karamar hukumar Lafia Alhaji Aminu Mu’azu Maifata ya bayyanawa manema labarai cewa zasu sharewa Gwamna Abdullahi Sule hawaye.
Alhaji Aminu Mu’azu Maifata shine Jagoran dake Jan ragamar Shugabannin Kananan Hukumomi a jihar Nasarawa.
Ya furta cewa Shugabannin Kananan hukumomi 13 da Masu rike da mukaman OBASIYA dake yan kunan raya kasa a fadin jihar. Sunyi alkawarin tabbatar da ganin Gwamna Abdullahi Sule ya kara maimaita mulki tsawon shekara hudu.
Aminu Mu’azu Maifata yace; Gwamna Abdullahi Sule yayi abin azo a gani. Ayyukan cigaba yana kuma kulawa da albashin ma’aikata akan lokaci.
Yace: ” Mu da mukafi kusa da jama’a da muke rike da kujerun Kananan hukumomi, munyiwa al’umman Kananan hukumomimu ayyukan alheri kamar yadda Gwamna Abdullahi Sule ya bukaci Mu kyautata, muyi ayyukan cigaba.
Aminu Mu’azu Maifata yayi kira ga al’umman jihar Nasarawa dasuyi tunani su kuma yi hangen nesa. Saboda Gwamna Abdullahi Sule cikin shekaru uku da rabi da yayi ya samar da cigaba mai garin yawa a biranai da karkara.
Ya bukaci al’umman jihar Nasarawa su kara baiwa Gwamna Abdullahi Sule goyon baya saboda kara samar da ayyukan cigaba jihar baki daya.
Hon. Aminu Mu’azu Maifata ya roki Allah kamar yadda Jam’iyyar APC ta fara gudanar da yakin niman zabe a garin Toto Allah yasa a gama duk zagayen da za ayi lafiya.