Jam’iyyar L.P da ADC sun marawa Gwamna Abdullahi Sule a Nasarawa

Jam’iyyar L.P da ADC sun nuna goyon baya ga Gwamnan Sule a Nasarawa

Daga Zubairu M. Lawal Lafia
Wasu daga cikin Mambobin Jam’iyyar L.P a jihar Nasarawa sun nuna goyon bayansu ga Gwamnan jihar Nasarawa kuma Dan takarar Jam’iyyar APC Injiniya Abdullahi Sule.
Wasu daga cikin Mambobin Jam’iyyar na L.P da suka hada da yan takarar Majalisu na Jam’iyyar da sauran masu fada aji, sun bayyana goyon baya su na cigaba da mulki karo na biyu ga Dan takarar Jam’iyyar APC a kujerar Gwamnan jihar Nasarawa.
Da karanta kasidar gaban manema Labarai a cibiyar yan Jaridu dake NUJ a Lafia. Rev. Agaba Kuje yace; tawagarsu na Mambobin Jam’iyyar L.P suna tare da Gwamna Abdullahi Sule.
Yace; abisa dalilinsu na goyon bayan Gwamna Abdullahi sule. Sunyi la’akar da yadda ya kawo cigaba cikin Shekara hudu a fadin Jihar Nasarawa.
Yace; Gwamna Abdullahi Sule ya Samar da hanyoyi biranai da karkara cikin fadin Jihar.
Gwamna Abdullahi Sule ya kawo zaman lafiya mai daurewa. Ya hada kan al’umman jihar Nasarawa ba tare da la’akari da bambamcin addini ko kabila ba.
Gwamna Abdullahi Sule yafi kowani Dan takarar Gwamna cancanta a fadin Jihar Nasarawa.
Haka zalika Dan takarar Gwamnan a Jam’iyyar ADC Hon. Godwin Williams Alaku da tawagarsa sums sun nuna goyon bayansu ga Gwamnan jihar Nasarawa kuma Dan takarar Jam’iyyar APC Injiniya Abdullahi Sule.
Jam’iyyun sunyi kira ga magoya bayansu dasu zabe Gwamna Abdullahi Sule a ranar Asabar 18 ga wata

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *