Da Dumiduminsa – An samu asarar rai da asarar dukiya a garin Bauchi a rikichin siyasa

Da Dumiduminsa – An samu asarar rai da asarar dukiya a garin Bauchi a rikichin siyasa

Daga Zubair M Lawal

Kazamin rikici ya barke tsakanin magoya bayan jam’iyyar People’s Redemption Party, PRP, da na jam’iyyar All Progressives Congress, APC a jihar Bauchi inda mutum daya ya rasa ransa kuma aka lalata kayayaki masu yawa.

majiyarmu ta  ruwaito cewa rikicin ya barke na a kusa da sha tale-talen Bauchi Club da ke titin Ahmadu Bello yayin da jam’iyyar na PRP ke shirin kaddamar da yakin neman zabenta.
ganau ya shaida afkuwar lamarin, cewa rikicin ya barke ne yayin da motar PRP ta tsaya a gaban ofishin magoya bayan jam’iyyar APC da ke kusa da shataletalen saboda lalacewa da tayi.

“Babu mamaki magoya bayan jam’iyyar na APC sunyi tunanin ‘yan PRP da gangan suka ajiye motar a gaban ofishinsu domin neman fada, hakan yasa rikici ya barke tsakaninsu,” inji wani da abin ya faru gabansa shi.

majiyarmu  ta ruwaito cewa motar da aka lalata kirar Honda Accord ne mai lamba DR-892-ABJ kuma wanda aka yiwa rauni dan jam’iyyar PRP sunansa Abdullahi. An garzaya dashi zuwa asibiti daga baya.

Da aka tuntube shi domin neman karin bayani, mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, DSP Kamal Abubakar ya ce kawo yanzu bai samu rahoton afkuwar rikicin ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *