Mukaddashin Gwamnan Nasarawa yayi kira ga Kiristochi da suyi adu’an zaman lafiya
Daga Zubairu Lawal
Mukaddashin Gwamnan jihar Nasarawa Dr. Emmanuel Agwadu Akabe yayi kira ga mabiya addinin kirista dasuyi amfani da ranar bikin kirsimeti wajen yiwa jihar Nasarawa da kasa adu’a.samun dauwamemen zaman lafiya.
Mukaddashin Gwamnan ya bayyana hakane cikin sakon murna da ranar bikin kirsimeti ga al’umman jihar Nasarawa.
Yace; ranar bikin kirsimeti ranace mai mahimmanci ga dukkan mabiya addinin kirista saboda ranarce aka haifi Yesu Al-masiyyu.
Dr. Emmanuel Akabe yace: duk kirista yana baiwa wannan ranar mahimmanci. Adan hakane yayi kira ga mabiya addinin kirista dasuyi amfani da koyarwar Yesu Al-masiyyu wajen tabbatar da zaman lafiya ga mabiya kowani addini.
Dr. Akabe yace: gudanar da adu’o’i Dan samun zaman lafiya da hadinkan al’umman jihar babban cigabane.
Yace: wannan ranar ranace ta nuna soyayya ga kowa da kowa. Kuma nabiya su kaunaci juna sun hadakai su taimaki juna domin addini ya koyar da zaman lafiya da kaunar junane a rayuwa.
Dr. Emmanuel Akabe yayi fatan Allah ya dawo da Gwamnan Abdullahi Sule gida lafiya daga tafiyar da yayi.