Mahara sunyi Garkuwa da Shugaban Karamar hukumar Akwanga
Wasu mahara daba a San suwayeba sunyi awan gaba da Shugaban Karamar hukumar Akwanga Alhaji Safiyanu Andaha.
Lamarin ya farune a ranar Littinin a yankin Andaha.
Makusantan Shugaban Karamar hukumar sun tabbatar da faruwan lamarin ga hukumar da manema labarai.
Sun tabbatar da maharar sunyi awan gaba da Shugaban Karamar hukumar akan titin Akwanga zuwa Andaha, a ranar bikin sabuwar shekara.
Duk da cewa Rundunar yan sandan jihar Nasarawa bata fitar da sanarwa manema labarai dangane da faruwan lamarin ba.
.