Ko kunsan dame Atiku ya dawo dashi daga Amurka
Daga Zubairu M lawal
Kwana uku da suka wuce alumman Nijeriya sun cika da mamakin ganin hotunan Atiku Abubakar a kasar Amurka dukda ikirarin day an adawa da kuma tsohon mai gidansa kuma tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo, ya taba yin ikirarin cewa, neman sa a ke yi a can za a kama shi kuma idan ya isa ya je din ya ga irin abinda zai faru da shi.
Saboda ana zarginsa da aikata lefin taimakawa wajen cin hanci.Duk da cewa, shi kansa Atiku ya yi karyata ikirarin kama shi da wannan laifi, amma ya taba bayyana cewa, ofishin jakadancin Amerika da ke Najeriya ya hana shi izinin shiga kasar bisa wani dalili wanda ba a bayyana ba.
A yayin da babban zaben kasar ke gabatowa, daya daga cikin abubuwan da jam’iyya mai mulkin Najeriya ke yakar Atikun da shi shi ne gazawarsa wajen iya shiga kasar ra Amurka, wanda hakan kullum ke nuna alamar kamar tsohon mataimakin shugaban kasar wani tsohon mai laifi ne wanda a ke neman sa ruwan a jallo a kasar waje.
Lokacin da a ka fara kishin-kishin din Atiku Abubakar zai samu izinin shiga Amerika a ’yan watannin baya, ministan yada labarai na Najeriya, Alhaji Lai Mohammed, ya soki lamirin kasar ta Amerika da cewa, muddin ta ba wa Atikun izinin shiga cikinta a wannan lokaci da babban zaben Najeriya ke matsowa, to tamkar ta na nuna cewa, shi ta ke goyon baya kenan a zaben, saboda me ya sa a baya ba ta ba shi ba, sai yanzu?
Yanzu dai za a iya cewa, karshen tika-tiki-tik, Atiku ya shiga Amerika ya wataya kuma har ya gudanar da taruka da wasu ’yan Najeriya mazauna kasar da kuma wasu jami’an gwamnatin kasar su ka yi tattaunawa a kan Najeriya. Babban abin tambaya a nan shi ne, shin a siyansance me zuwan Atiku Amerika ya ke nufi a wannan lokaci da zabe ya karato? Shin hakan zai sa ya samu karin kuri’a daga wajen ’yan Najeriya masu zabe? Shin hakan ya na nufin alakar gwamnatin Najeriya a karkashin jagorancin Muhammadu Buhari ta yi rauni da Amerika ne har su na tunanin yiwuwar kawo sauyi, kamar yadda minsitan labarai Lai Mohammed ya nuna damuwarsa?
Shin Obasanjo, wanda ya fara tona batun, ya taba yiwa Atiku karya kenan? Shin wata cuwa-cuwa a ka je a ka hada, wacce ta sa Amerika ta dawo ta kyale Atiku ya shiga kasarta ne? shin Buhari bai gamsar da Amerika ba ne ko kuwa dai su na ganin rashin bai wa Atiku izinin shiga kasar ya na nufin sun tauye wa Atiku wani abu kenan a siyasance, wanda ba sa so a yi mu su kallon nuna bambanci?
To, ko ma dai mene ne amsoshin wadannan tambayoyi, za a iya cewa, Atiku ya karya wancan kofi kuma ya nuna cewa, lallai jam’iyyar APC da dan takararta su tashi tsaye wajen kokarin lashe zaben 2019, domin wannan damar da dan takarar PDP ya sami cikin bazata ta na nuni da alamun cewa, za a iya yi mu su sakiyar da ba ruwa kenan .