Zancen karshe Mata Zai tafi Valencia ko Juventus
Daga Ibrahim Lawal
Dan wasa Juan Mata yana daf da yin zaman karshe da kungiyar kwallon kafa ta Manchester United don sanin yadda makomarsa zata kaya, ko zai tsawaita ta ko kuma zai kara gaba yakoma wata kungiyar.
Mata wanda a yanzu haka yake cikin watanni shida na karshen kwantiraginsa, wanda hakan ke nufin yana da ikon fara tattauna kana ya amince da tafiya wata kungiyar idan wa’adin zamansa a Manchester United ya kare.
Kawo yanzu dai tsohuwar kungiyarsa ta Valencia da kuma Juventus tuni suka nuna sha’awarsu ta daukar dan wasan Amma duk da shi Mata yana jin dadin zamansa a United, sai dai su Manchester na son rage masa yawan adadin kudin da dan wasan yake dauka a sati na £170,000.
Mata dai na son cigaba da zama a kungiyar amma dai ba ya samun damar buga wasanni sosai, domin kuwa a cikin wasanni biyar da kungiyar ta buga ya samu dammar buga wasanni biyu ne kacal karkashin sabon mai horaswa Solskjaer.
Tuni dai aka bayyana cewa wakilin dan wasan wanda kuma shine mahaifinsa zai tattauna da hukumomin kungiyar domin ganin an cimma matsaya akan kwantaragin dan wasan kafin ya sake sabuwar yarjejeniya.
Mata dai yana cikin shekara ta biyar a Manchester United tun bayan daya koma kungiyar a watan Janairun shekara ta 2014 a lokacin tsaohon kociyan kungiyar Dabid Moyes bayan yabar Chelsea.