Bubu wanda zai iya Maye Gurbin Ronaldo a kwallon kafa
Inji wani Babban Dan wasa
Daga Ibrahim Lawal
Tsohon Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Nani, ya ce zai yi wahala a iya samun wanda zai iya maye gurbin zakarar Dan wasa kamar Cristiano Ronaldo a duniya nan gaba.
Nani ya bayyana haka ne a wata hira da yayi da manema labarai inda yace Ronaldo Dan wasa ne na daban kuma nasarorin da yake samu har yanzu sune suka banbanta shi da ragowar ‘yan wasa a duniya.
Arsenal ta na Son Gareth Bale Me zakace?
Arsenal da Real Madrid da Barcelona ke zawarcinshi ?
Yayin da yake zantawa da manema labarai dangane tasirin sauyin shekar Ronaldo zuwa Juventus daga Real Madrid, Nani ya ce, kungiyar Juventus za ta cigaba da marawa Ronaldo baya domin kare mutuncinsa, dan gane da zargin aikata fyaDe da wata mata ke yi masa anan gaba.
Nani, wanda suka buga wasa da Ronaldo a Manchester United da kasar Portugal ya kuma bayyana cewa bayan Juventus Ronaldo zai iya zuwa wata kungiyar sanann kuma yaci gaba da jan zarensa.
Nani wanda yanzu yake buga wasa a kungiyar kwallon kafa ta Sporting Lisbon ya bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid tayi kuskuren siyar da Ronaldo a irin wannan lokacin da basu da yawa a duniya.
A karshe ya bayyana cewa yana fatan Ronaldo zai sake buga gasar cin kofin duniya nan da shekaru uku domin yaja ragamar tawagar ‘yan wasan kasar ga nasara inda yace babu abinda Ronaldo bazai iyaba a duniyar kwallon kafa.