Dubban alumma ke kwarara zuwa sansanin gudun hijira ta Pulka
Daga Safeeya Halilu
Akalla dubban alumma ne ke tururuwa zuwa sansanin gudun hijira dake yankin Pulka dake kan iyaka da qasar Kamaru .
A labarin da hukumar kula da yangudun hijira ta duniya ta bayar cewa wanan sansanin ta Pulka yana amsan dubannin jama’a da suka tsero daga garuruwansu da Rikicin addini kona Kabilanci ya deideita.
Hukumar tace . dole yasa suka fara tanadar magunguna cuta kala kala masamman na tarin-fuka .
Sansanin yan gudun hijira na Pulka na karban dubban alumma a koda yaushe
Tace; wanan sansanin yana daya daga cikin manyan sansanin dake samum kwararan yan gudun hijira daga gurare dabam dabam saboda yadda yake a kan iyaka .
Hukumar tace; a shekarar 2018 anfi samun yawaitar yan gudun hijira a wanan sansanin idan yanzu sukeda kiddidiga samada mutum 8750 akasarinsu matane da yara Qananan da tsofafi. A sanadiyar hakane sansanin yayi fama da qarancin ruwansha da abinchi da magunguna.
A shekarar 2017 samada mutum 3700 suka fado cikin sansanin bazato ba tsammani daga Nijeriya,inda sukazo cikin mawuyacin hali da niman agaji na gaggawa. Hakan yasanya muka kafa matsugunai na wucingadi saboda matsalar ruwansama da makamancin hakan.
Daga watan Yuli zuwa Satumba sansanin ya samu karbuwar yan gudun hijira masu yawa dole ta sanya aka kafa ofishin bibiyar bukatun yan gudun hijirar. Aka fara tunanin samarda karin kayayakin bukatuwarsu kamar Magani ruwansha abinchi kayan sanyawa dana kwanciya .
Kungiyoyin agaji sun hada kai saboda duba damuwar yan gudun hijirar, kamar kungiyar Oxfam da kungiyar samarda abinchi ta duniya da kungiyar Samarar da kula da yan gudun hijira ta duniya da kungiyar kula da Qananan yara ta duniya. Saboda asamar da kayayakin bukatuwa da sansanin ke bukata .
Tuni aka samar da wadannan abubuwa , sauran da ya rage aka ajiyesu saboda gaba da kuma yan gudun hijirar dake zuwa.
An kuma yi amfani da Qananan Barikokin Soje wajen tantancen sabbin yan gudun hijirar dake zuwa bayan tantancesu sai a turasu cikin sansanin.
Bayan watanni da magance wancan matsalolin da suka hada da kiwon Lafiya da sauransu. yanzu sansanin ta sake fadawa cikin makamanciyar wancan matsalar saboda karuwar wasu yan gudun hijirar da yawansu ya haura 3000. Ga kuma matsalar rashin ishahsen tsaro. Haka zalika tana famada rashin ishashen gurin da za’a samarda wasu karin guraren kwanciya a sansanin gashi kuma alumma karuwa sukeyi