RA’AYIN EDITA NA JARIDAR THISDAY* A KAN CIGABA DA TSARE SHAIKH EL-ZAKZAKY

*RA’AYIN EDITA NA JARIDAR THISDAY*
A KAN CIGABA DA TSARE SHAIKH EL-ZAKZAKY

Daga Abubakar Musa

*Ci gaba da tsare Shaikh El-Zakzaky ba bisa ka’ida ba ne*

Duk da ikirari mai jan hankali da gwamnatin tarayya ta yi kwanan nan cewa tana kashe kimanin kudi Naira miliyan 3.5 a duk wata wajen ciyar da Shaikh Ibraheem El-Zakzaky, Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya (IMN), wanda yake a tsare tun watan Disambar 2015, mabiyansa suke ta yin muzaharori a-kai-a-kai a Abuja, suna neman a sake shi. Kamar yadda muka sha bayyanawa a baya, dole ne gwamnati ta rika la’akari da abin da ka iya biyo baya ta fuskacin tsaro, in aka bar wannan mutumi da ake tsare da shi ba bisa ka’ida ba ya mutu a tsare.

Shehin Malamin dai an kama shi ne a ranar 14 ga watan Disamban 2015 bayan hatsaniyar da ta auku tsakanin jama’arsa da sojojin Nijeriya a yayin shirin wani taronsu a garin Zariya, a jihar Kaduna. A yayin wannan hatsaniya, almajiransa 347, ciki har da ‘ya’yansa uku sojojin suka kashe. Da ma a watan Yulin shekarar 2014, sojojin sun kashe masa wasu yaran guda uku. Duk kuwa da wadannan kashe-kashen, gwamnati ta ci gaba da nuna halin da aka san ta da shi na rashin bin doka a kan al’amarin.

Yana da kyau a lura cewa, a ranar 2 ga watan Disamban 2016, Mai shari’a Gabriel Kolowole na babbar kotu da ke Abuja ya bayar da umurnin a saki El-Zakzaky da mai dakinsa, tare da nuna cewa, ci gaba da tsare su, ba wai kawai karya doka ba ne, amma kuma babban hatsari ne ga wannan kasa. Ya yi gargadin cewa, “Idan mai kara ya rasu, alhali yana a tsare …. Hakan zai iya haifar da wasu mace-macen na ba gaira ba sabat.” Bayan la’akari da haka, Alkalin ya ba da umarnin a sake su cikin kwanaki 45. Ya kuma bayar da umarni ga hukumar DSS su biya tarar kudi har Naira miliyan 25 ga kowanne, El-Zakzaky da kuma matarsa.

To, sai dai har bayan shekara biyu bayan yanke wannan hukunci, El-Zakzaky da matarsa suna a tsare duk kuwa da koke a kan hakan daga ciki da wajen kasar nan. Misali, kungiyar Amnesty International ba ta yi wani boye-boye ba wajen tsage gaskiyar da ta fada a kan hatsarin abin da gwamnati ta aikata: “Idan har gwamnati da gangan ta ki bin umarnin kotunanta, wannan na yin nuni da rashin girmamawa, da yin karan tsaye mai hatsari ga tsarin mulki irin na bin doka.” Ta bayyana. Tun da dai shi ke da alhakin komai, dole mu fada wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa, muna fa a cikin mulkin dimokaradiyya ne, kuma irin rashin mutunta umarnin kotu da ya zama wani alami na gwamnatinsa ba abin alheri ba ne ga al’ummarmu.

To, sai dai rashin bin umurnin kotu na wannan gwamnati ba wai kawai a kan tsare El-Zakzaky ya tsaya ba. Tsohon mai ba da shawara kan harkokin tsaro na kasa, Kanar Sambo Dasuki mai ritaya, wanda ake tuhuma da karkatar da kudi kimanin Dalar Amurka biliyan 2.1, wanda aka ware domin sayen makamai a shekarar 2015, har yanzu yana a tsare duk da umurnin kotu sabanin hakan. Gwamnatin ma dai ba kotunanta ne kawai ba ta bin umurninsu ba, tana sane da gangan ta ki bin umurnin kotun kungiyar kasashen yammacin Afirka (ECOWAS) wadda a ranar 4 ga watan Oktobar 2016 ta bayyana cewa tsare Dasuki ba kan ka’ida ba ne, kuma karya doka ne. Kotun ma ta bayyana sake kama shi a shekarar 2015 bayan an sake shi da cewa, rainin wayo ne ga dimokaradiyya.

Gwamnatin Tarayya bai kamata ta ci gaba da boyewa bayan ikirarinta na “Tsaron kasa” ba, ta ci gaba da aikata abin da yake ba bisa ka’ida ba, kuma ya saba wa tsarin mulki, wanda ci gaba da tsare El-Zakzaky da matarsa ke nunawa. Don haka muna kira ga Shugaban kasa, wanda sai da ya yi rantsuwar zai kare tsarin mulki da ya bi umurnin kotu ya ba da umurnin a sake su. Gwamnatin Tarayya bai kamata ta ci gaba da tsare wadannan ma’aurata biyu ba, wadanda ba a kama su da aikata kowane irin laifi ba.

*Yau Juma’a 01 ga Maris, 2019 aka buga Ra’ayin a jaridar Thisday.*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *