BABBAN MAGANA- Sanata Adekwe ya maka Gwamna Al-makura gaban kotu

Sanata Adekwe ya maka Gwamna Al-makura gaban kotu

Daga Zubair M Lawal

Sanata mai wakiltar Nasarawa ta kudu Sanata Sulaiman Adekwe ya qalubalanci Gwamna Al-makura gaban Shari’a.

Sanatan yana kalubalantar Gwamnan ne game da yadda yace; an gudanar da magudin zaben da ya gudana a ranar 23/2/2019.

Sanata Sulaiman Adekwe na jam’iyyar PDP Wanda ya kwashe shekara 12 yana wakiltar yankin Nasarawa ta kudu inda ta hada qananan hukumomi biyar . Lafia, Doma, Keana, Awe Obi.
Adekwe yace; Gwamna Umar Tanko Al-makura bai ci zabe ba . wanan abune da yake zahiri.

Muna da ingantatun hujoji da suka tabbatar mana da yin nasara a zabe, da yake zantawa da manema labarai bayan gabatar da kara a gaban kotun sauraran qararakin zabe dake zama a garin Lafia a shekara jiya .

Adekwe yace; ” munyi nasara mun lashe zabe a garuruwan Doma Obi Lafia dama keana . Amma aka murde mana da karfin tsiya . Anyi amfani da hukumar zabe aka dinga kashe mana kuri’a a gurare da dama “.

Damuwarsu kawai su kwace nasarar mu ko ta halin qaqa. ” ya qara da cewa , anyi amfani da jami’an tsaro da hukumar zabe wajen sauke sakamakon zabe mai yawa saboda anga muyin nasara” babu inda za’ayi ace Al-makura yayi nasara a wanan zaben saboda alumma basu zabe shi ba.

Yace; wanan ba shine na farko ba da ake yimin makirci a zabe kuma idan na kai kotu Allah yabani nasar nake karbar kayata ba.

“Adekwe yace; da Al-makura yayi nasara a wanan zaben na gaskiya da gaskiya da bazan kalubalanci nasararsa a gaban kotu ba sai dai na tayashi murna .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *